Karya ta kare: Yansandan Najeriya sun yi ram da wani gungun yan fashi su 6 da binidigunsu

Karya ta kare: Yansandan Najeriya sun yi ram da wani gungun yan fashi su 6 da binidigunsu

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya ta musamman dake yaki da yan fashi da makami, FSARS, sun yi nasarar damke wasu gagararrun yan fashi da makamisu shidda a garin Owerri na jahar Imo, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewar dama yan fashin sun dade suna addabar al’ummar jahar, don haka hukumar Yansandan jahar ta shiga farautarsu ba dare ba rana, inji kwamishinan Yansandan jahar, Dasuki Galadanci.

KU KARANTA: PDP: Bafarawa ya yi watsi da duk wani tayin sulhu da sauran yan takarar shugaban kasa

Karya ta kare: Yansandan Najeriya sun yi ram da wani gungun yan fashi su 6 da binidigunsu

Yan fashi
Source: Depositphotos

Kwamishinan yace sun samu nasarar kama yan fashin ne da safiyar Lahadi, 2 ga watan Satumba, inda ya bayyana sunayensu kamar haka; Onyebuchi Uruaku mai shekaru 62, Michael Chigozie 20, Ifeanyi Uchenna 21, Ugochukwu Ejiniogu 28, da Chinonso Obiakor mai shekaru 32.

Haka zalika kwamshina Dasuki yace sun kwato makamai daga hannun yan fashin kamar haka, kananan bindigu guda biyu, alburusai da dama da wata jaka cike da tabar wiwi.

Kwamishinan ya yaba da kokarin da jami’an Yansandan jahar Imo keyi wajen kawar da ayyukan yan ta’adda da masu aikata miyagun laifuka, sa’annan ya kara da cewa zasu ninka kokarin da suke yi don yaki da miyagun ayyuka, musamman a yayin bukukuwan karshen shekara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel