Filato ta sake kamawa da wuta: An kashe mutane 11 da raunata wasu 12

Filato ta sake kamawa da wuta: An kashe mutane 11 da raunata wasu 12

- Wasu ‘yan binda da ba a san ko su waye ba sun kai hari a yankin Lopandet Dwei a karamar hukumar Jos ta kudu

- Maharan sun kasha mutane 11 tare da raunata wasu 12

- Hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewar tuni ta tura jami’anta yankin domin dakile wasu hare-haren da kan iya biyo bayan harin ‘yan bindigar

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari yankin Lopandet Dwei a karamar hukumar Jos ta kudu tare da kasha mutane 11 da raunata wasu 12, kamar yadda hukumar ‘yan sanda ta tabbatar a yau, Litinin.

Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Filato, DSP Terna Tyopev, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewar ‘yan bindigar sun kai harin ne a daren ranar Lahadi, 2 ga watan Satumba.

Filato ta sake kamawa da wuta: An kashe mutane 11 da raunata wasu 12

Ibrahim Idris, shugaban rundunar 'yan sanda
Source: Facebook

A jiya ne da misalin karfe 8:30 na dare muka samu rahoton cewar ‘yan bindiga sun kai hari yankin Lopandet Dwei Du dake karamar hukumar Jos ta kudu.

“Ba tare da wani bata lokaci ba muka tura jami’an ‘yan sanda yankin. Sai dai kafin zuwan jami’an mu tuni ‘yan bindigar sun harbi wasu mutane kafin su gudu,” a kalaman Tyopev.

DUBA WANNAN: 2019: Sai mun tika Buhari da kasa - Mata 6 dake takarar shugaban kasa

Kakakin ya kara da cewa sun garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti tare da jibge jami’an ‘yan sanda a yankin domin dakile wasu hare-haren da kan iya biyo bayan harin ‘yan bindigar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel