Taron FOCAC 2018: Manyan abubuwa 5 da Buhari ya fadi a China

Taron FOCAC 2018: Manyan abubuwa 5 da Buhari ya fadi a China

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar, 1 ga watan Satumba ya isa Beijing, kasar China domin halartan taron hadin gwiwar China da Afrika (FOCAC 2018).

Shugaba Buhari wadda ya kasance shugaban kungiyaar ECOWAS yayi jawabi ga shugabannin kasar China da na Afrikada kuma wakilan kasuwanci a taron.

Legit.ng ta tattaro wasu manyan abubuwa da shugaban kasar ya fadi a jawabinsa.

KU ARANTA KUMA: Babu wani tantancewa da za’a yiwa Saraki, Atiku, Kwankwaso da sauransu a yanzu

Taron FOCAC 2018: Manyan abubuwa 5 da Buhari ya fadi a China

Taron FOCAC 2018: Manyan abubuwa 5 da Buhari ya fadi a China
Source: UGC

1. Dangantaka tsakanin China da ECOWAS

Shugaba Buhari yace akwai kyakwyawar alaka a tsakanin China da kasashen Afrika. Yace halartan taron da shugabanni da jihohin ECOWAS suka yi ya nuna cewa akwai alaka mai kyau tsakaninsu da China.

Ya kuma yi godiya ga Shugaba Xi Jinping akan alkawarin ginawa hukumar sakatariya da yayi.

2. Rawar ganin da ECOWAS take tawa a Afrika

Shugaban kasar ya kuma ce yankin ECOWAS sune keda kaso 30% na yawan mutane a yankin Afrika.

3. Inganta tattalin arziki

Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa mambobin kungiyar ECOWAS na aiki akan manufofin da tsare-tsare don inganta ci gaban kasashensu da habbaka tattalin arziki.

4. Zuba hannun jarin China a Afrika na Yamma

Shugaba Buhari a madadin mambobin kasashen ECOWAS ya yi godiya ga gwamnatin China kan ci gaba da zuba jari a yankin Afrika tare da kokarin gina makoma mai inganci.

5. Nemawa mutanen ECOWAS Visa

Shugaba Buhari ya kuma nemi alfarman visa ga mutanen yankin Afrika yan kasuwa da dalibai dake neman ziyartan China.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel