Wasu mambobin APC sunyi watsi da jan kunnen da akayi masu sun gabatar da taro ba bisa doka ba

Wasu mambobin APC sunyi watsi da jan kunnen da akayi masu sun gabatar da taro ba bisa doka ba

- Wasu mambobin jam'iyyar APC sunyi kunnen uwar shegu da gargadin shugaban jam'iyyar

- Sun gudanar da haramtaccen taro akan hukuncin da jam'iyyar ta yanke game da zaben fidda gwani

- Mafi akasarin wadanda suka halarci taron shugabannin kananan hukumomi ne

Wasu mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun gana a Abuja, sa’o’i kadan bayan shugaban jam’iyyar yayi gargadi akan gudanar da taron.

Mukaddashin sakataren jam’iyyar na kasa, MistaYekini Nabena, ya gabatar da sanarwa da farko, inda ya ja hankali akan abunda ya bayyana akan haramtaccen taro da wasu mambobin jam’iyyar suka shirya gabatarwa a ranar Lahadi a babban birnin tarayya.

Wasu mambobin APC sunyi watsi da jan kunnen da akayi masu sun gabatar da taro ba bisa doka ba

Wasu mambobin APC sunyi watsi da jan kunnen da akayi masu sun gabatar da taro ba bisa doka ba
Source: Depositphotos

A sanarwan, Mista Nabena ya bayyana cewa za’a gudanar da taron ne domin ganin laifin hukuncin da jam’iyyar ta yanke kan zaben fidda gwani akan zaben 2019.

Ya ci gaba da gargadin cewa sakamakon irin wannan ganawa zai kasance ba bisa ka’ida ba sannan ya bukaci mambobin jam’iyyar da suyi watsi da shi.

KU KARANTA KUMA: Babu wani tantancewa da za’a yiwa Saraki, Atiku, Kwankwaso da sauransu a yanzu

Dukkanin wadanda suka halarci taron basu yadda suyi Magana da manema labarai ba kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Sai dai an tattaro cewa wasu daga cikin wadanda suka halarci ganawar sun kasance shugabannin jam’iyyar na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel