2019: Yawan yan takara ba zai tarwatsa PDP ba - Shekarau

2019: Yawan yan takara ba zai tarwatsa PDP ba - Shekarau

- Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa yawan adadin yan takarar kujerar shugaban kasa da ke neman tikitin jam’iyyar a zaben 2019 ba zai tarwatsa jam’iyyar ba

- Yace hakan alamun nasara ne ga jam'iyyar

- Shekarau ya jadadda cewa Allah ne zai zabi wanda zai yi jagora kuma su kansu yan takaran sun san cewa mutun guda ne zai wakilci jam'iyyar

Tsohon ministan ilimi kuma dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Democratic Party (PDP), Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa yawan adadin yan takarar kujerar shugaban kasa da ke neman tikitin jam’iyyar a zaben 2019 ba zai tarwatsa jam’iyyar ba.

Shekarau ya bayyana hakan a wani jawabi da yayi bayan ziyarar ta’aziya ga gwamnan jihar Bayelsa, Hon Seriake Dickson akan rasuwar mahaifiyarsa a garin Toru-Orua dake karamar hukumar Sagbama na jihar.

2019: Yawan yan takara ba zai tarwatsa PDP ba - Shekarau

2019: Yawan yan takara ba zai tarwatsa PDP ba - Shekarau
Source: Twitter

Yace yawan adadin yantakara a jam’iyyar adawa ta PDP alamu ne na nasara, cewa abun da yafi muhimmanci shine yadda suka hade kansu sannan suka fuskanci yakin neman zabensu a matsayin yan uwan juna.

A cewarsa, Allah ne zai zabi wadda zai yi jagora sannan kuma cewa dukkanin yan takarar na sane da cewar mutun daya ne zai iya lashe tikitin wakiltan PDP a zaben shugaban kasa wadda aka shirya gabatarwa a shekara mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Jami’in soja ya soki wani dan makaranta saboda bashi a Lagas (hoto)

A halin da ake ciki, shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayi bayanin dalilin da yasa ba’a kaddamar da wani kwamiti da zai tantance yan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar ba tukuna.

Baya ga yan takarar kujerar shugaban kasa, jam’iyyar bata ambaci wani kwamiti da zai yi duba ga takardun sauran yan jam’iyya.

Tuni dai yan takara da dama sun yanki fam din takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar inda suke jira a kaddamar da kwamitin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel