Ban ma sani ba ko a PDP nake har yanzu – Tsohuwar mataimakiyar gwamna

Ban ma sani ba ko a PDP nake har yanzu – Tsohuwar mataimakiyar gwamna

- Tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Akwa Ibom tace bata da masaniya kan jam'iyyar da take a yanzu

- Ana dai rade-radin cewa Misis Ebe ta koma APC daga PDP

- Ta ce idan lokacin yayi za'a sani idan ma ta bar PDP

Tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Akwa Ibom, Valeria Ebe ta bayyana cewa bata san ko har yanzu tana a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ko akasin hakan ba.

Ana ta rade radin cewa Misis Ebe ta sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Ban ma sani ba ko a PDP nake har yanzu – Tsohuwar mataimakiyar gwamna

Ban ma sani ba ko a PDP nake har yanzu – Tsohuwar mataimakiyar gwamna
Source: Depositphotos

A lokacin da majiyarmu ta Premium Times ta tuntube ta a yammacin ranar Lahadi, ga watan Satumba ko ta sauya sheka kamar yadda ake yayatawa, tsohuwar mataimakiyar gwamnan tace, “ban sani ba tukuna. Ina a gidana. Idan na bari, zaku ji”.

A wani lamari na daban, Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayi bayanin dalilin da yasa ba’a kaddamar da wani kwamiti da zai tantance yan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar ba tukuna.

KU KARANTA KUMA: Sai da Obasanjo ya tuhume ni akan goyon bayan sake fasalin lamuran kasar - Atiku

Baya ga yan takarar kujerar shugaban kasa, jam’iyyar bata ambaci wani kwamiti da zai yi duba ga takardun sauran yan jam’iyya.

Tuni dai yan takara da dama sun yanki fam din takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar inda suke jira a kaddamar da kwamitin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel