Shirin fitar da ‘Yan takara ya fara jawo rigima tsakanin ‘Ya ‘yan APC

Shirin fitar da ‘Yan takara ya fara jawo rigima tsakanin ‘Ya ‘yan APC

- An yi wani mugun rikici tsakanin ‘Ya ‘yan APC a Jihar Adamawa kwanan nan

- Wasu ‘Yan daba ne su ka kai wa wasu manyan Jam’iyyar APC mai mulki hari

- Ana zargin cewa Gwamnan Jihar ne ba ya son ayi ‘Yan tike wajen zaben 2019

Shirin fitar da ‘Yan takara ya fara jawo rigima tsakanin ‘Ya ‘yan APC

APC na neman kawo sabon tsari na tsaida 'Yan takara a 2019
Source: Depositphotos

Mun samu labari yau dinnan cewa wani mummunan rikici ya barke tsakanin wasu manyan Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa a karshen makon nan. Ana tunani rigimar ba ta rasa nasaba da zaben fitar da gwani da za ayi.

Wasu ‘Yan iskan gari ne da ake tunani su na tare da Mai Girma Gwamna Muhammadu Jibrilla Bindow su kayi kokarin jawo fitina domin nuna rashin amincewar su da tsarin da Uwar Jam’iyyar APC ta ke shirin kawowa.

Jam’iyyar APC na kokarin yin amfani da zaben kato-bayan-kato wajen fitar da ‘Yan takarar ta a zaben 2019. Gwamnonin APC da dama dai ba su yi na’am da wannan tsari ba wanda hakan ya fara kawo tashin hankali a wasu wurare.

KU KARANTA: Abin da ya taba hada ni rigima da Obasanjo - Atiku

Daily Trust ta rahoto cewa wasu ‘Yan daba da ke goyon bayan Gwamna Bindow sun rusa ofishin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal. Hakan yayi sanadiyyar raunuka da kuma barnata motoci da dama.

‘Yan Tawaren Jam’iyyar APC a Adamawa karkashin Dimas Ezra sun zargi Gwamna da kitsa wannan aiki. Manyan APC a Jihar irin su Murtala Nyako, Babachir Lawal da Nuhu Ribadu su na tare da bangaren Taware na Ezra.

Wadannan 'Yan daba sun fasa taron da aka shirya ne bayan sun ji ana kokarin amincewa da zaben kato-baya-kato wajen bada tutar Jam'iyya. Shi dai Gwamna Muhammadu Jibrilla yace ko kadan babu hannun sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel