A yanzu babu wani yanki dake karkashin kulawar Boko Haram a Najeriya - Buhari

A yanzu babu wani yanki dake karkashin kulawar Boko Haram a Najeriya - Buhari

- Shugaba Buhari ya bayyana cewa babu wani yanki a kasar dake karkashin ikon yan ta’addan Boko Haram a yanzu

- Ya ce an cimma wannan nasara ne a karkashin gwamnatinsa da taimakon hukumomin tsaro

- Buhari ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro na iya bakin kokarinsu domin ganin karshen ta'addanci a kasar

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu wani yanki a kasar dake karkashin ikon yan ta’addan Boko Haram a yanzu.

Ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 2 ga watan Satumba, a Beijing, kasar China yayinda yake bayyana wasu nasarori da gwamnatinsa ta samu a lokacin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya mazauna kasar.

Shugaban kasar ya danganta nasarorin ga ayyukan da hukumomin tsaro suka gudanar wajen yakar ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.

A yanzu babu wani yanki dake karkashin kulawar Boko Haram a Najeriya - Buhari

A yanzu babu wani yanki dake karkashin kulawar Boko Haram a Najeriya - Buhari
Source: Twitter

Yace: “Idan zaku tuna mun nemi takarar zabe na karshe da ya gudana akan lamura uku, wadanda suka hada da tsaro musamman a yankin Arewa masu gabas.

“A baya yan Boko Haram su shafe kusan kananan hukumomi da dama a jihar Borno amma a yanzu babu kowanne a hannunsu."

Ya kuma bayyana cewa yan ta’addan sun samu wasu dabarun kaddamar da ayyukan ta’addancinsu.

KU KARANTA KUMA: Sai da Obasanjo ya tuhume ni akan goyon bayan sake fasalin lamuran kasar - Atiku

“Sun samo wasu hanyoyin kaddamar da hare-harensu ta hanyar amfani da kananan yara, musamman mata da kuma kai hari cocina, masallatai da kasuwanni," inji shi.

Ya jadadda cewa hukumomin tsaro na iya bakin kokarinsu akan lamarin ta’addanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel