Rahoto ya bankado dalilin rushewar Cocin Najeriya da aka gina fiye da shekara 100 da suka wuce

Rahoto ya bankado dalilin rushewar Cocin Najeriya da aka gina fiye da shekara 100 da suka wuce

- A jiya, Lahadi, ne wata Coci, St. Paul Catholic Church, dake karamar hukumar Okpe a jihar Delta ta rushe tare da kasha mutane masu yawa da kuma jikkata wasu

- Kwamishinan aiyuka a jihar, Cif James Augoye, ya bayyana cewar Cocin ta rushe ne yayin kokarin fadada gininta da aka yi a shekara 100

- Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, y ace gwamnatinsa zata dauki nauyin yiwa wadanda suka samu raunuka magani

A jiya, Lahadi, ne wata Coci, St. Paul Catholic Church, dake Adagbarasa ta karamar hukumar Okpe a jihar Delta, ta rushe yayin da jama’a ke gudanar da bautar ranar Lahadi.

Kwamitin da gwamnan jihar gwamna Ifeanyi Okowa na jihar ya kafa karkashin kwamishinan aiyuka, Cif James Augoye, ya fitar da wani rahoto dake cewar Cocin ta rushe ne saboda kokarin fadada gininta na asali da aka yi shekara 100 da suka wuce.

Rahoto ya bankado dalilin rushewar Cocin Najeriya da aka gina fiye da shekara 100 da suka wuce

Rahoto ya bankado dalilin rushewar Cocin Najeriya da aka gina fiye da shekara 100 da suka wuce
Source: Facebook

Rahoton kwamitin ya kara bayyana cewar kokarin fadada tsohon ginin da ruwan sama ya saka shi yin laushi ga kuma nauyin masu ibada, sune suka jawo rushewar ginin Cocin.

DUBA WANNAN: 'Yan Najeriya sun yiwa Atiku shagube a kan zubar da hawaye

A yayin da muka dauki alkawarin biyan kudin magungunan duk wadanda suka ji ciwo, muna son yin kira ga jama’a da kungiyoyi da su tabbatar sun samu izini daga hukumomin gwamnati kafin fara gina wani wuri da jama’a da yawa zasu yi amfani da shi,” a cewar Cif Augoye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel