Gwamna Ambode bai da niyyar barin Jam’iyyar APC – Hadimin Shugaba Buhari

Gwamna Ambode bai da niyyar barin Jam’iyyar APC – Hadimin Shugaba Buhari

Mun samu labari cewa Gwamna Akinwumi Ambode ya bayyana cewa sam bai da niyyar barin Jam’iyyar APC mai mulki kamar yadda ake ta jita-jita cikin ‘yan kwanakin nan a Najeriya.

Gwamna Ambode bai da niyyar barin Jam’iyyar APC – Hadimin Shugaba Buhari

Ambode yace idan ba a sani ba yana tare da Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

Wani Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamna Akinwumi Ambode na Legas ya fada masa cewa babu gaskiya a maganar da ake yi na cewa zai sauya sheka daga Jam’iyyar APC zuwa wata Jam’iyyar.

Bashir Ahmad wanda yana cikin masu ba Shugaba Buhari shawara ya bayyana cewa ya fadawa Gwamna Ambode cewa Jaridun Najeriya su na yada cewa zai tsere daga APC. Ahmad yace Gwamnan yayi dariya yace yana nan tare da Buhari.

KU KARANTA: PDP ba za ta tantance 'Yan takaran ta ba tukuna

Hadimin na Shugaban kasar ya bayyana wannan ne a shafin sa na Tuwita wanda hakan ya kawo karshen rade-radin da aka yi na cewa Gwamnan zai bar APC. A cikin ‘Yan kwanakin nan dai APC na rasa manyan ‘Ya ‘yan ta a Yankin zuwa ADC.

Yanzu haka Shugaba Buhari ya tafi taron kusan mako guda zuwa Kasar China tare da wasu Gwamnonin APC. A tawagar Shugaban kasar dai akwai Gwamna Akinwumi Ambode na Legas da kuma Gwamnonin Imo, Bauchi da kuma Jigawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel