Gaskiyar Buhari ce ta ke jawo Shugabannin Duniya zuwa Najeriya – Ministan labarai

Gaskiyar Buhari ce ta ke jawo Shugabannin Duniya zuwa Najeriya – Ministan labarai

Ministan yada labarai na kasar nan Lai Mohammed ya bayyana cewa Kasashen Duniya na shigowa Najeriya ne domin ganin irin kokarin Gwamnatin Shugaba Buhari musamman a bangaren sha’anin tsaro da kuma gina abubuwan more rayuwa.

Gaskiyar Buhari ce ta ke jawo Shugabannin Duniya zuwa Najeriya – Ministan labarai

Minista Lai Mohammed yace kasashen waje na neman kulla alaka da Buhari
Source: Twitter

Lai Mohammed yake cewa a Ranar Laraba ne Firayim Ministar Birtaniyya Theresa May ta zo Najeriya, bayan nan kuma Shugaba Angela Merkel Jamus ta zo kasar. Ministan yace Najeriya ta shiga yarjejeniya dabam-dabam da kasashen.

Ministan yada labaran ya zanta da ‘Yan jarida a gidan Talabijin na NTA a jiya Lahadi inda yake cewa Shugabannin Duniya na zuwa Kasar nan ne saboda irin gaskiyar Shugaban kasa Buhari da kuma saukin kasuwanci da hulda da Najeriya.

Mohammed ya kuma bayyana cewa Najeriya ta samu nasarori iri-iri kamar a fagen tattali wajen dabbaka tsarin asusun bai-daya na TSA wanda ya taimakawa Gwamnatin kasar. Lai yace Buhari yayi kokarin babbako da tattalina arzikin Najeriya.

KU KARANTA: Atiku Abubakar ya samu karin goyon baya daga Yarbawan Najeriya

Ministan kasar ya kuma yi magana game da siyasar Kasar inda yace yana goyon bayan amfani da ‘yan-tike wajen fitar da ‘Yan takarar APC. Mohammed ya kuma ce ficewa da Bukola Saraki yayi daga APC alheri ne gare su a Jihar sa ta Kwara.

A makon jiya ne Firayim Ministar Birtaniya Theresa May ta kawo ziyara Najeriya. Mun kawo maku ribar da Najeriya ta samu daga wannan babban ziyara daga Shugabar ta Turai idan ba ku manta ba wanda daga ciki akwai samun aikin yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel