Ministan shari’a ya bukaci kotu da tayi watsi da karar da aka shigar kan tsige Saraki

Ministan shari’a ya bukaci kotu da tayi watsi da karar da aka shigar kan tsige Saraki

Alkalin alkalai kuma ministan shari’a, Mista Abubakar Malami ya kalubalanci hukuncin babban kotun tarayya na sauraron karar dake bukatar a dakatar da tsige Dr Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Ministan shari’an ya bukaci babban kotun da tayi watsi da karar da tsoffin sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Rafiu Adebayo da Isa Misau. Suka shigar a gabanta.

Ya bayyana yan majalisan guda biyu da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin makirai, inda yace lallai sun gaza gabatar da wani kwakwaran hujja akan lamarin ba.

Ministan shari’a ya bukaci kotu da tayi watsi da karar da aka shigar kan tsige Saraki

Ministan shari’a ya bukaci kotu da tayi watsi da karar da aka shigar kan tsige Saraki
Source: Depositphotos

Yace masu karan sun gaza nuna yadda tsige Saraki zai shafi yancin su, inda ya zarge su da zakewa akan lamarin fiye da wanda abun ya shafa.

Hakan na kunshe ne a takardan jayayya da Malami ya cika inda yake adawa da karar day an majalisa biyu suka shigar inda suke rokon kotu da ta hana duk wani yunkuri na bude majalisa ta karfin tuwo tare da kokarin tsige Saraki daga matsayinsa.

KU KARANTA KUMA: 2019: ‘Yan Najeriya sun yiwa Atiku shagube a kan zubar da hawaye

Yan majalisan biyu dake wakiltan Kwara ta Kudu da Bauchi ta tsakiya sun yi zargin cewa wasu jiga-jigai daga tsohuwar jam’iyyarsu ta APC karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole da ministan shari’a na shirin yin amfani da hukumomin tsaro wajen tsige Saraki daga matsayinsa na shugaban majalisar dattawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel