An kama mu ne saboda Allah ya kaddara – Yan fashi

An kama mu ne saboda Allah ya kaddara – Yan fashi

- An damke yan fashi da makami a jihar Neja

- Sun nuna rashin nadamar wannan aiki da sukeyi

- An raunata mutum daya daga cikinsu

Wani dan fashi da makami, Hussaini Dikko, wanda jami’an yan sanda suka damke tare da abokan aikinsa, yace da ba’a kamasu ba baccin Allah ya kaddara za’a kama su.

Jami’an yan sandan jihar Neja, sun damke Hussaini Dikko, Usman Dikko da Usman Umar a rgan Fulanin Gufanri a karamar hukumar Bussa da ke jihar.

An samu rahoton cewa yan fashin sun addabi mazauna Wawa, New Bussa, kafin hukuma ta cika hannu da su.

An kama mu ne saboda Allah ya kaddara – Yan fashi

An kama mu ne saboda Allah ya kaddara – Yan fashi
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Babban hadimin gwamnan jihar Akwa Ibom ya koma APC

Jaridar Northern City News ta tattaro cewa a ranan Lahadi, yan fashin sunyi musayar wuta da jami’an yan sanda inda jami’ai suka samu galaba a kansu.

Hussaini ya bayyanawa manema labarai cewa yaransa sunyi harbe-harbe da yan sanda ne domin tsira.

“Mun bude musu wuta ne domin mu samu arcewa amma sai suka raunata daya daga cikinmu yayin musayar wuta har suka kama su.”

“Allah ya kaddara za;a kama su, saboda haka babu abinda wani zai yi. Mun rungumi kaddara, saboda haka doka tayi aikinta,”

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Muhammadu Abubakar, ya bayyana irin makaman da aka samu hannunsu. Kana za’a gurfanar da su a kotu idan aka kammala bincike

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel