Babban hadimin gwamnan jihar Akwa Ibom ya koma APC

Babban hadimin gwamnan jihar Akwa Ibom ya koma APC

- Jam'iyyar PDP ta sake babban rashi a jihar Akwa Ibom

- Hadiman gwamnan biyar sun bar gwamnatinsa tun fita Godswill Akpabio daga PDP

Babban hadimin gwamnan jihar Akwa Ibom kan duba ayyuka, Utibe Idem, ya sauya sheka daga jamiyyar PDP zuwa APC.

Wannan shine hadimin gwamna Udom Emmanuel na biyar da suka fita daga jam’iyyar PDP a makonnin da suka gabata.

Hadimin gwamnan da sauran mutanen da suka sauya sheka sun samu kyakkyawar tarba daga shugaban jam’iyyar APC na jihar, Ini Okopido, a karamar hukumar Nsit Ubium a wani babban taro da aka shirya domin karrama Umana Umana, tsohon dan takaran gwamnan jihar.

KU KARANTA: Najeriya, UN da wasu manyan kasashe 2 zasu lalubo hanyar kawo karshen Boko Haram a Turai

Idem ya ce ba ya nadaman ajiye aikinsa a matsayin hadimin gwamnan domin komawa jam’iyyar APC.

Yace: “Ina fada da babban murya na bar tsohon gida. Daga yau, ni da iyalai na mambobin APC ne. APC wajen zama ne,”

A bangarensa, Umana ya ce mutanen jihar Akwa Ibom sun nuna soyayyarsu ga jam’iyyar APC kamar yadda aka gani a rijistan mambobi a jihar.

Ya jaddada cewa da irin wannan soyayya da ake yiwa APC, Ko shakka babu za’a samu nasara a zaben 2019. Ya tabbatarwa masoyansa cewa nasarar da aka hanasu a 2015, za su samu a 2019.

Umana ya godewa shugaba Muhammadu Buhari kan baiwa yan jihar AKwa Ibom mukamai cikin gwamnatinsa, cewa wadannan mukamai musamman na diraktan NDDC, ya taimakawa cigaba a jihar sosai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel