Kungiyar Afenifere za ta marawa Atiku baya a 2019 domin ya sauya fasalin Najeriya

Kungiyar Afenifere za ta marawa Atiku baya a 2019 domin ya sauya fasalin Najeriya

- Shugaban Kungiyar Afenifere, Ayo Adebanjo yace su na tare da Atiku Abubakar

- Adebanjo yace za su marawa Atiku baya ne saboda zai canzawa Najeriya fasali

Kungiyar nan ta Yarbawa ta Afenifere ta bayyana cewa za ta marawa Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar baya a zaben 2019. Shugaban Kungiyar Ayo Adebanjo ya fadi haka wajen wani taro da aka yi a makon jiya.

Kungiyar Afenifere za ta marawa Atiku baya a 2019 domin ya sauya fasalin Najeriya

Afenifere tayi amanna da tafiyar Atiku Abubakar
Source: Depositphotos

Kamar yadda labari ya zo mana, Kungiyar Afenifere za ta goyi bayan Atiku Abubakar ne saboda aniyar sa na yi wa tsarin kasar nan garambawul. Ayo Adebanjo ya bayyana wannan jiya a Legas lokacin da aka gayyaci Atiku wani taro.

Kungiyar tace ba tun yau Atiku ya fara yin wannan kira na sauyawa Najeriya fasali ba. Adebanjo yace fiye da shekaru 10 da su ka wuce kenan Atiku yana fafatuka wajen ganin an yi wa tsarin Najeriya garambawul domin cigaban kasar.

KU KARANTA: Ni na fi dacewa da tikitin takarar Shugaban kasa a PDP - Bafarawa

Afenifere na goyon bayan sakewa Najeriya fasali kuma tana ganin babu wanda ya dace da wannan aiki irin Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku. Atiku dai yana cikin ‘Yan sahun gaba na masu takarar Shugaban kasa a karkashin PDP.

Atiku lokacin da yake na sa jawabin yace bai taba ganin Najeriya ta shiga cikin wani hali na hadari kamar wannan lokacin ba tun da ya fara siyasa. Atiku yace cikin watanni 6 da hawan sa mulki zai sakewa Najeriya fasali idan yayi nasara a 2019.

Atiku yace tun yana Mataimakin Shugaban kasa yake wannan kira na canza tsarin Najeriya wanda har hakan ta hada su rikici da Shugaban kasa Olusegun Obasanjo bayan yayi wani jawabi yana mai wannan kira a Legas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel