Najeriya, UN da wasu manyan kasashe 2 zasu lalubo hanyar kawo karshen Boko Haram a Turai

Najeriya, UN da wasu manyan kasashe 2 zasu lalubo hanyar kawo karshen Boko Haram a Turai

An shirya wani babban taro a tsakanin kasashen Najeriya, Jamus, Norway da majalisar dinkin duniya a birnin Berlin dake kasar Jamus akan lalubo hanyoyin kawo karshen yakin ta’addanci na Boko Haram, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Za’a fara wannan taro ne daga ranar Litinin 3 ga watan Satumba zuwa Talata 4 ga wata, kuma zai mayar da hankali zuwa ga mawuyacin halin da yan gudun hijira suke ciki, kare fararen hula, dakile faruwar hare hare da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin tafkin Chadi.

KU KARANTA: PDP: Bafarawa ya yi watsi da duk wani tayin sulhu da sauran yan takarar shugaban kasa

Najeriya, UN da wasu manyan kasashe 2 zasu lalubo hanyar kawo karshen Boko Haram a Turai

Yan gudun hijira
Source: Depositphotos

Haka zalika a yayin taron za’a binciko hanyar da za’a tattaro kudaden da za’a tallafa ma yan gudun hijira dake Najeiriya, Nijar, Chadi da Kamaru tare da mayar dasu matsuguninsu, kudaden da suka kai dala biliyan 1.56.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wakilin Najeriya a wannan babban taro, jakadan Najeriya a majalsar dinkin Duniya shine Farfesa Tijjan Bande, kuma yace Najeriya ta shirya wani tsarin kashe dala biliyan 6.7 don kula da matsalolin yan gudun hijra.

“Ina kira ga masu ruwa da tsaki dasu kara kaimi wajen tabbatar da ganin taron na Berlin ya cimma manufar da aka shirya shi akai.” Inji Bande.

Bugu da kari Bande yayi kira da aka cigaba da hadin gwiwa tsakanin Najeriya da sauran kasashen dake yankin tafkin Chadi, da kuma kasashe da kungiyoyi masu zaman kansu dake taimakawa da kudade, hadin gwiwar dayace ya ja hankalin majalisar dinkin Duniya.

Shima jagoran aikin taimako na majalisar dinkin Duniya dake Najeriya, Edward Kallon yace har yanzu Najeriya na cikin mawuyacin hali, “Akalla mutane miliyn 10.2 ne rikicin Boko Haram ta shafa a jihohi uku dake yankin Arewa maso gabas.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel