2019: Jam'iyyar PDP zata kori wasu 'yan takara

2019: Jam'iyyar PDP zata kori wasu 'yan takara

- Jam'iyyar PDP reshen jihar Legas ta ce zata kori duk dan takarar da ya yi amfani da 'yan ta'adda gabanin zaben 2019

- Jam'iyyar ta bukaci 'yan takara a karkashinta da su guji wani hali da kan iya jawowa PDP bacin suna

- Sakataren yada labaran jam'iyyar a jihar Legas, Mista Taofik Gani, ya sanar da cewar PDP ta bude sayar da takardun takara

Reshen PDP na jihar Legas ya gargadi masu takara a jam'iyyar da su guji nuna zakuwa ko tayar da hankali a kokarinsu na kai wa ga nasara a zaben shekarar 2019.

Kazalika PDP tayi gargadin korar duk dan takarar da ya ki yin biyayya ga dokokin jam'iyyar.

Jam'iyyar tayi wannan jawabi ne a wani sako da ta aike ga manema labarai mai dauke da saka hannun sakataren yada labarai a jihar Legas, Mista Taofik Gani.

2019: Jam'iyyar PDP zata kori wasu 'yan takara

Jam'iyyar PDP zata kori wasu 'yan takara
Source: Twitter

Mista Gani ya sanar da cewar jam'iyyar PDP a jihar Legas ta fara sayar da takardun takara na kujerun gwamna, Sanata, majalisar wakilai da ta dokoki.

Sai dai jam'iyyar bata bayyana adadin kudin takardun tsayawa takarar ba.

DUBA WANNAN: Adadin sojojin da 'yan Boko Haram suka kashe a jihar Borno ya karu

PDP ta sanar da cewar masu son yin takarar majalisar dokokin jihar Legas zasu karbi takardun takara a ofishin jam'iyyar na jiha bayan nuna takardar shaidar biyan kudi.

Sannan ta kara da cewar 'yan takarar gwamna da Sanata da majalisar wakilai zasu karbi takardun takara a ofishin uwar jam'iyya na kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel