Jihohin Najeriya da PDP za ta gamu da cikas game da 2019

Jihohin Najeriya da PDP za ta gamu da cikas game da 2019

Mun samu labari cewa rikicin siyasa na nema ta rutsa da babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a wasu Jihohin Arewa. Wadannan Jihohi sun hada da Kano da kuma Kogi, Sokoto da Jihar Benuwai.

Jihohin Najeriya da PDP za ta gamu da cikas game da 2019

Ortom na neman yi wa 'Yan PDP karfa-karfa a Benuwai
Source: Depositphotos

1. Kano

A Jihar Kano kun ji labari cewa an fara samun takaddama tsakanin ‘Yan Kwankwasiyya da kuma manyan PDP a Jihar irin su Malam Ibrahim Shekarau, Aminu Wali, Bello Hayatu Gwarzo da sauran su. Shekarau da Kwankwaso su na neman Shugaban kasa

2. Sokoto

Da alamu dai PDP za ta shiga rikici a Jihar Sokoto bayan Gwamnan Jihar Aminu Tambuwal ya sauya sheka. Tambuwal zai samu matsala wajen takarar Shugaban kasa, sannan kuma akwai rikici tsakanin sa da tsohon Gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa.

KU KARANTA: Rikici na nema ya barke a PDP a Jihar Kano

3. Benuwai

A Jihar Benuwai ma dai za a buga rikici a 2019. Gwamna Ortom ya sauya sheka daga APC kwanaki inda yake neman zarcewa a PDP. Hakan ya kawo rabuwar kai a PDP wanda ya ja har wasu ‘Yan takara su ka fara komawa Jam’iyyar APC a Jihar.

4. Kogi

A Jihar Kogi ana samun rabuwar kai tsakanin ‘Ya ‘Yan Jam’iyyar PDP. Sanata Dino Melaye na APC ya koma PDP inda zai nemi Jam’iyyar ta basa tikitin sake tsayawa kujerar Sanata a Jihar. Sai dai hakan na neman kawo rikici a Jam’iyyar adawar a Kogi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel