Alamu sun bayyana karara na faduwar PDP tun kafin zaben 2019 - APC

Alamu sun bayyana karara na faduwar PDP tun kafin zaben 2019 - APC

- Jam'iyyar APC ta ce guiwar jam'iyyar adawa ta PDP ya yi sanyi tun gabanin zaben 2019

- APC ta ce damuwar da PDP ta yi na yadda APC zatayi zaben fitar da gwani alama ce ta karayar zuciya da kuma sallamawa ga nasarar zaben

- Jam'iyyar ta roki yan Nigeria da su ci gaba da marawa gwamnatin Buhari baya, wajen inganta rayuwar al'umar kasar

Jam'iyya mai mulki ta APC, a cikin wata sanarwa a yau lahadi, ta ce: "La'akari da mambobin jam'iyyar APC sama da Miliyan 13 da sukayi rejista, da kuma kusoshin siyasar kasar da ke nuna goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Buhari, alamu na nuna cewa PDP ta karaya da tsarin zaben fitar da gwani da APC ta dauka na yin kato-bayan-kato."

Jam'iyyar ta APC ta yi mamakin yadda jam'iyyar PDP ta damu kwarai da tsarin zaben kato-bayan-kato da APC ta dauka a zaben fitar da gwani, ta na mai cewa hakan alama ce da ke nuna cewa PDP ta sallamawa APC tun kafin zaben 2019.

Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun sakataren watsa labarai na jam'iyyar a Abuja, Mr. Yekini Nabena Ag., ta ce, yin zaben fitar da gwani ta hanyar kato-bayan-kato, na daga cikin hanyoyin gudanar da adalci; baiwa yan takara damar baje kolinsu; magance matsalar cin hanci ga jami'an gudanar da zabe; da kuma baiwa mambobin jam'iyyar damar zabar wanda su ke so.

Alamu sun bayyana karara na faduwar PDP tun kafin zaben 2019 - APC

Alamu sun bayyana karara na faduwar PDP tun kafin zaben 2019 - APC
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Tsadar tikiti: Da alama APC za ta rasa yan takara a zaben fitar da gwani

A cewar sanarwar: "Muna sane da cewa irin tsarin da APC ta dauka na yin zaben kato bayan kato a fitar da gwani zai zama banbarkwai ga PDP, jam'iyyar da kowa ya san dama can bata iya gudanar da shugabancin cikin gida, da kuma rashin baiwa mambobinta damar zabar wanda suke so.

"APC jam'iyya ce da ke ci gaba a kullum, kuma zata ci gaba da kawo sauye sauye da cika alkawuran canjin da tayiwa yan Nigeria."

Daga karshe, sanarwar ta roki yan Nigeria da su ci gaba da marawa gwamnatin shugaba Buharinbaya, a kokarin sake gina kasar da ta ke yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel