Da dumin sa: Shugaba Buhari yayi wasu muhimman nade-nade guda 4

Da dumin sa: Shugaba Buhari yayi wasu muhimman nade-nade guda 4

- Shugaba Buhari yayi wasu muhimman nade-nade guda 4

- Nade naden na da alaka ne da kamfanin nan na gwamnatin tarayya dake bugawa tare da tsare takardun sirri

- Yanzu Alhaji Abbas Umar Masanawa ne shugaban kamfanin

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari mun samu labarin cewa ya amince da wasu sabbin nade-nade guda hudu da suke da alaka da kamfanin nan na gwamnatin tarayya dake bugawa tare da tsare takardun sirri watau Nigerian Security Printing and Minting Company.

Da dumin sa: Shugaba Buhari yayi wasu muhimman nade-nade guda 4

Da dumin sa: Shugaba Buhari yayi wasu muhimman nade-nade guda 4
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Dogara ya kammala shirin yiwa APC babbar illa

Kamar yadda muka samu, Shugaba Buhari din ya nada Alhaji Abbas Umar Masanawa a matsayin babban manajan Daraktan kamfanin tare kuma da wasu manyan daraktocin sa su biyu.

Legit.ng ta samu cewa sabbin Daraktocin da shugaba Buhari ya amince da su sun hada da Abubakar Sule Minjibir, Tunji Kazeem da kuma Chris Orewa.

Shi dai Alhaji Abbas wanda yake dan asalin jihar Katsina ne, kafin wannan matsayin nasa shima babban Darakta ne a kamfanin da ke kula da harkokin kudi, kasuwanci da kuma tsare-tsare.

A wani labarin kuma, Rahotannin dake fitowa daga wasu makusantan kakakin majalisar wakillan Najeriya Yakubu Dogara ya kammala dukan shirye-shiren sa na ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki yana jiran lokacin da yafi dacewa ne kawai ya ayyana matsayar ta sa.

Binciken majiyar mu dai ya tabbatar mana da cewa duk da yake har yanzu bai fadi matsayar ta sa ba amma kusan dukkan alamun da ka iya nuna hakan sun tabbata a tattare da shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel