Sojoji 3 da fararen hula 4 aka kashe a wani harin kunar bakin wake

Sojoji 3 da fararen hula 4 aka kashe a wani harin kunar bakin wake

- Akalla mutane 7 ne wani harin kunar bakin wake ya lakume rayuwarsu a birnin Mogadishu, kasar Somaliya

- Shugaban hukumar kula da lardin Mogadishu, Mr. Salah Omar Hassan, shi ya bayyana hakan tare da cewa adadin mutanen na iya karuwa

- Har zuwa yanzu dai babu wata kungiyar ta'addanci da ta dauki alhakin kai harin, sai dai gwamnatin kasar ta dora alhakin akan kungiyar Al-Qaeda

Akalla sojoji 3 tare da fararen hula 4 a yau lahadi aka kashe a wani harin kunar bakin wake, da akayi amfani da mota wajen tayar da abun fashewa a birnin Mogadishu, kasar Somaliya.

Mai magana da yawun hukumar kula da lardin Mogadishu, Mr. Salah Omar Hassan, ya ce daga cikin wadanda suka mutu akwai kananan yara guda 2, da kuma samari 2.

"Zamu sanar da manema labarai halin da ake ciki, amma yanzu iya abinda muka tattara kenan daga wadanda harin ya shafa" a cewar Mr. Hassan, ya na mai kara cewa an samu mutane 14 da suka jikkata.

Motar wacce ta ke dauke da ababen fashewa, ta yi bindiga ne a gundumar Howlwadag, daya daga cikin gundumomi 17 na birnin Mogadishu. Ta fashe a lokacin da ta yi karo da katangar wani gini a yankin.

KARANTA WANNAN: Rundunar soji ta karyata rahoton cewa Boko Haram ta kai hari a sansanin soji dake Borno

Kusan karfin fashewar ya fi shafar wata makarantar Islamiya da kuma masallacin da ke kusa da ofishin hukumar kula da lardin na Mogadishu.

"Jaruman sojojin da suke bada tsaro a yankin ne sukayi kokarin hana motar shiga harabar ginin, inda motar ta bugi katangar ginin, a nan take ta fashe" a cewar mai magana da yawun hukumar.

Ana sa ran adadin wadanda harin ya shafa ya kara yawa, la'akari da gidaje masu yawa da ke kusa da ginin da aka kaiwa haroin, wadanda fashewar motar ta lalata su. Jim kadan bayan fashewar motar, an ji karar harbe harben bindiga, alama da ke nuni da cewa yan bindiga sun kai hari a kwaryar garin.

Sai dai har zuwa yanzu babu wata kungiyar ta'addanci da ta yi ikirarin kai harim, amma gwamnatin Somaliya ta saba alakanta hare haren da ake kawowa kasar da kungiyar ta'addanci ta Al-Qaeda da ke da nasaba da Al-Shabaab.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel