Naka sai naka: Buhari zai kashe Dalar Amurka biliyan 6.7 don farfado da yankin Arewa maso gabas

Naka sai naka: Buhari zai kashe Dalar Amurka biliyan 6.7 don farfado da yankin Arewa maso gabas

- Naka sai naka: Buhari zai kashe $6.7 biliyan don farfado da yankin Arewa

- Wakilin Najeriya na din-din-din a majalisar dinkin duniya Farfesa Tijjani Bande shine ya sanar da hakan

- Gwamnatin Najeriya ta nemi taimako don cimma burin nata

Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta ce ta kammala wani cikakken daftari dake dauke da tsare-tsaren yadda za'a habaka yankin Arewa maso gabas da 'yan ta'addan Boko Haram suka kassara.

Naka sai naka: Buhari zai kashe Dalar Amurka biliyan 6.7 don farfado da yankin Arewa maso gabas

Naka sai naka: Buhari zai kashe Dalar Amurka biliyan 6.7 don farfado da yankin Arewa maso gabas
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wani na kusa da Buhari ya tsage gaskiya

Wakilin Najeriya na din-din-din a majalisar dinkin duniya Farfesa Tijjani Bande shine ya sanar da hakan a lokacin da yake tattaunawa da wasu mahalarta taron lalubo hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da kuma farfado da tafkin Cadi na majalisar.

Legit.ng ta samu cewa Farfesa Tijjani Bande yace daftarin da gwamnatin tarayyar ta kammala zai lakume akalla Dalar Amurka biliyan 6.7 don farfado da yankin tare da sake tsugunnar da wadanda rikicin na Boko Haram ya kora daga gida.

Haka zalika Farfesa Tijjani Bande ya kuma bukaci dukkan masu hannu da shuni da kuma kasashen duniya gami da kungiyoyi da su taimaka wajen cikar wannan burin.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar sojin saman Najeriya dake a cikin rundunar hadakar fatattakar 'yan Boko Haram ta 'Lafiya Dole ta sanar da samun gagarumar nasara akan 'yan ta'addan a garin Zari dake a kan iyaka da tafkin Cadi, jihar Borno.

Jami'ain hulda da jama'a na rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola shine ya sanarwa da manema labarai hakan a ranar Juma'ar da ta gaba a garin Abuja babban birnin tarayya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel