Fasalin kasa: Atiku yayi aman wuta, yayi kaca-kaca da mataimakin Shugaban kasa Osinbajo

Fasalin kasa: Atiku yayi aman wuta, yayi kaca-kaca da mataimakin Shugaban kasa Osinbajo

- Atiku yayi kaca-kaca da mataimakin Shugaban kasa Osinbajo

- Ya zarge shi da rashin sanin inda kasa ta dosa

- Atiku yace zai sauya fasalin Najeriya idan ya zama shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma fitaccen dan siyasa dake neman tikitin takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2019 ya bayyana cewa sam mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo bai ma gama fahimtar Najeriya ba.

Fasalin kasa: Atiku yayi aman wuta, yayi kaca-kaca da mataimakin Shugaban kasa Osinbajo

Fasalin kasa: Atiku yayi aman wuta, yayi kaca-kaca da mataimakin Shugaban kasa Osinbajo
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Sule Lamido ya fadin dalin da ya sa PDP yakamata ta tsaida shi takara

Atiku dai yana maida martani ne game da kalaman Osinbajo din da yayi a lokacin da yake tattaunawa da wasu 'yan Najeriya a kasar Amurka inda yace wai sauya fasalin kasar baya daya daga cikin matsalolin Najeriya.

Legit.ng ta samu sai dai a cikin wata sanarwar manema labarai da ofishin Kamfe na Atiku din ya fitar, ya bayyana cewa ba abun mamaki bane don hakan ta fito daga bakin sa domin basu ma san matsalar kasar ba daman.

Fitaccen dan siyasar dake zaman jigo a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kuma kara da cewa shi idan ya zama shugaban kasar Najeriya zai sauya fasalin kasar ta yadda zai ragewa gwamnatin tarayya karfin ikon ta.

A wani labarin kuma, Wasu rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu suna nuni ne da cewa wasu makusantan Shugaba Muhammadu a fadar shugaban kasa sun nan sun yi nisa wajen shirya kutungwuilar maido da Lawal Daura da aka kora aikin sa.

Majiyar dai wadda jaridar Vanguard tace kusa take da shugaban kasar ta ce makusantan na Shugaba Buhari basu jin dadin irin sauye-sauyen da sabon shugaban riko na hukumar tsaron farin kayan na DSS mai suna Mathew Seiyefa yake yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel