Amurka ta rage yawan man da take saye daga Najeriya da kaso 62 cikin 100

Amurka ta rage yawan man da take saye daga Najeriya da kaso 62 cikin 100

- Amurka ta rage yawan man da take saye daga Najeriya da kaso 62 cikin 100

- Wannan dai babban nakasu ne ga tattalin arzikin Najeriya

- Najeriya ta dogara kacokan kan danyen man fetur din ta

Adadin danyen bakin man da kasar Amurka ke saye daga kasar Najeriya da ke a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari a yanzu haka yayi kasa da ganga miliyan uku a duk wata adadin da bai taba kai hakan ba a duk 'yan kwanakin nan.

Amurka ta rage yawan man da take saye daga Najeriya da kaso 62 cikin 100

Amurka ta rage yawan man da take saye daga Najeriya da kaso 62 cikin 100
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wani dan sanda a Najeriya ya kashe direba saboda Naira 10

Wannan dai kamar yadda masana tattalin arzikin kasa suka yi fashin baki ba abu bane da zai haifarwa da kasar da mai ido musamman ma yanzu da tattalin arzikin kasar ke farfadowa.

Legit.ng ta samu cewa a baya dai anyi lokacin da kasar ta Amurka take sayen miliyoyin gangunan mai daga Najeriya wanda kuma hakan ya taimaki kasar sosai.

Kasar Najeriya dai kafin yanzu ta dogara ne kacokam ga kudaden da take samu wajen sayar da danyen mai zuwa kasashen waje kamar su Amurka da sauran kasashen nahiyar turai.

A wani labarin kuma, Wasu rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu suna nuni ne da cewa wasu makusantan Shugaba Muhammadu a fadar shugaban kasa sun nan sun yi nisa wajen shirya kutungwuilar maido da Lawal Daura da aka kora aikin sa.

Majiyar dai wadda jaridar Vanguard tace kusa take da shugaban kasar ta ce makusantan na Shugaba Buhari basu jin dadin irin sauye-sauyen da sabon shugaban riko na hukumar tsaron farin kayan na DSS mai suna Mathew Seiyefa yake yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel