Ta tabbata: Yakubu Dogara ya kammala shire-shiren ballewa daga APC

Ta tabbata: Yakubu Dogara ya kammala shire-shiren ballewa daga APC

- Yakubu Dogara ya kammala shire-shiren ballewa daga APC

- An ce ya dade yana kulle-kullen sa

- Hadiman sa sune suka fara ficewa da APC din

Rahotannin dake fitowa daga wasu makusantan kakakin majalisar wakillan Najeriya Yakubu Dogara ya kammala dukan shirye-shiren sa na ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki yana jiran lokacin da yafi dacewa ne kawai ya ayyana matsayar ta sa.

Ta tabbata: Yakubu Dogara ya kammala shire-shiren ballewa daga APC

Ta tabbata: Yakubu Dogara ya kammala shire-shiren ballewa daga APC
Source: UGC

KU KARANTA: Wani gwamna na shirin ficewa daga APC

Binciken majiyar mu dai ya tabbatar mana da cewa duk da yake har yanzu bai fadi matsayar ta sa ba amma kusan dukkan alamun da ka iya nuna hakan sun tabbata a tattare da shi.

Legit.ng ta samu cewa daya daga cikin manyan hadiman sa kuma diya ga fitaccen dan siyasar nan Marigayi Cif MKO Abiola watau Rinsola Abiola a cikin 'yan kwanakin nan ne ta fita daga jam'iyyar ta APC.

Haka zalika wani lamari da ya daurewa kowa kai shine na yadda aka nemi Sifika Dogara aka rasa a wajen taron jiga-jigan jam'iyyar ta APC da ya gudana a satin da ya gabata.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma fitaccen dan siyasa dake neman tikitin takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2019 ya bayyana cewa sam mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo bai ma gama fahimtar Najeriya ba.

Atiku dai yana maida martani ne game da kalaman Osinbajo din da yayi a lokacin da yake tattaunawa da wasu 'yan Najeriya a kasar Amurka inda yace wai sauya fasalin kasar baya daya daga cikin matsalolin Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel