Bai dace Shugaba Buhari ya dauki Gwamnoni da Sanatoci wajen taron Kasar China ba – Adamu Garba

Bai dace Shugaba Buhari ya dauki Gwamnoni da Sanatoci wajen taron Kasar China ba – Adamu Garba

Adamu Garba wanda yana cikin masu neman kujerar Shugaban kasa ya fito ya soki Shugaba Muhammadu Buhari game da daukar ‘Yan siyasa da yayi cikin Tawagar sa zuwa Kasar China.

Bai dace Shugaba Buhari ya dauki Gwamnoni da Sanatoci wajen taron Kasar China ba – Adamu Garba

Shugaba Buhari ya tafi Kasar China inda zai yi kwanaki 6 da wasu Gwamnonin APC
Source: Depositphotos

Malam Adamu Garba wanda Matashi ne mai harin kujerar Shugaban kasa Buhari a 2019 yayi Allah-wadai da abin da fadar Shugaban kasar tayi kwanan nan yayin da Shugaban Najeriya Buhari ya kai wata babban ziyara zuwa Kasar Sin.

Garba ya nuna takaicin sa na daukar Iyalin Shugaban kasa da kuma ‘Yan siyasan APC da aka yi zuwa Kasar Sin watau China. Shugaba Buhari ya tafi taron ne da Gwamnoni da wasu Ministoci har da ma da wasu fitattun Sanatocin Jam'iyyar APC.

A cewar Matasahin ‘Dan siyasar, Mutanen Kasar Sin din su da wahalar sha’ani don haka yake ganin ya kamata ace ne Shugaba Buhari ya tafi da kwararru wadanda su ka san harkokin kasar waje amma sai ya kare da daukar ‘Yan siyasa.

KU KARANTA: Timi Frank yace Buhari ya tafi China ne don a tsige Saraki a Majalisa

A tawagar Shugaban kasar dai akwai Gwamnoni 4 na Legas, Imo, Bauchi da kuma Jihar Jigawa da Ministoci har 9 wanda su ka hada da Rotimi Amaechi, Babatunde Fashola, Udo Udoma, Ibe Kachikwu, Muhammad Musa Bello da sauran su.

Har da kuma wasu manyan Sanatocin APC dai Shugaban Kasar ya tafi wannan karo. Daga cikin Sanatocin da aka fita da su akwai Abdullahi Adamu, George Akume, Aliyu Wamakko da kuma Godswill Akpabio wanda ya bar PDP kwanan nan.

Adamu Garba yaba ganin bai dace ace Shugaban na Najeriya Buhari ya dauki manyan 'Yan APC da Iyalin sa wajen wannan taro na kusan mako guda mai muhimmancin gaske ba domin kuwa ba ziyarar siyasa bace ko ta taron ganin dangi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel