Ko kadan ba na fargabar zaben da ke cike da adalci - Shugaba Buhari

Ko kadan ba na fargabar zaben da ke cike da adalci - Shugaba Buhari

- Daga birnin Beijing, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu dalilin da zai sa ya ji tsoron gudanar da sahihin zabe

- Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da yan Nigeria mazauna kasar Sin

- Buhari ya bukace su, da su zabi jam'iyyar APC a babban zaben 2019 da ke gabatowa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, 2 ga watan Satumba, ya bayyana cewa babu dalilin da zai sa ya ji tsoron zaben 'a kasa a tsare a raka' a zaben 2019.

Da ya ke jawabi a birnin Beijing, kasar Sin, a lokacin da ya ke zantawa da yan Nigeria mazauna kasar, Buhari ba zai ji tsoron a gudanar da sahihin zabe ba, kasancewar irin zaben nan ya bashi nasara har ya zama shugaban kasar.

Idan za'a iya tunawa, Shugaban kasar ya tsaya takara har sau 4 bai samu nasara ba har sai a zaben 2015, inda ya lashe zaben shugaban kasar karkashin jam'iyyar APC.

Da ya ke bayyana wannan matsaya ta shi, Buhari ya ce: "Ni na san halin da na shiga, na tsaya takara har sau 4, amma karo na hudun, kimiya da fasaha suka taimaka, inda akayi amfani da na'urar tantance masu kada kuri'a, wanda hakan ne ya bani nasara a wancan lokaci"

Ko kadan ba na fargabar zaben da ke cike da adalci - Shugaba Buhari

Ko kadan ba na fargabar zaben da ke cike da adalci - Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Ruwan sama ya rusa makabarta da hana mutane binne gawa a jihar Katsina (Hotuna)

Legit.ng a bayan nan ta ruwaito cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta sha alwashin samun nasara a zaben 2019 na shugaban kasar mai zuwa. Domin samun wannan nasarar, wasu kusoshi daga jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa PDP.

Daga cikin wadanda suka bayyana sha'awarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa karkashin PDP akwai: Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Sanata Bukola Saraki, Atiku Abubakar, Sule Lamido, Alhaji Atahiru Bafarawa, da dai sauransu.

A jam'iyyar APC kuwa, har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayyana kudirinsa na tsayawa takara a jam'iyyar.

Da wannan ne ma dai shugaban kasa Buhari a yau, a birnin Sin, ya bukaci yan Nigeria mazauna kasar, da su marawa gwamnatinsa baya da kuma zabar jam'iyyar APC a babban zaben 2019 da ke gabatowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel