Ina da Digiri sama da 10 don haka ni na dace in rike Najeriya – Dankwambo

Ina da Digiri sama da 10 don haka ni na dace in rike Najeriya – Dankwambo

Wani ‘Dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP watau Ibrahim Hassan Dankwambo ya fito ya nuna cewa shi ya cancanta a zaba a Najeriya a zabe mai zuwa na 2019.

Ina da Digiri sama da 10 don haka ni na dace in rike Najeriya – Dankwambo

Gwamna Dankwambo yace yana da Digiri fiye da 10 a Duniya
Source: Depositphotos

Tsohon Akanta Janar na Najeriya kuma Gwamnan Gombe Dr. Ibrahim Hassan Dankwambo wanda yana cikin masu takarar kujerar Shugaban kasa a Jam'iyyarPDP yace yana da duk abin da ‘Dan takara yake bukata wajen mulkin Najeriya.

Dr. Dankwambo mai shekaru 56 yace yayi karatun Boko na gaske kuma yayi aikace-aikace a wurare da-dama tun yana matashi don haka yake ganin duk inda ‘Dan takara ya kai ya kai. Gwamnan na Jihar Gombe ya dace ya mulki kasar nan.

Gwamnan yayi wannan jawabi ne a shafin sa na Tuwita kwanan nan inda ya bayyana cewa yana da Digiri sama da 10 a fannoni dabam-dabam. A dalilin haka ne ‘Dan siyasar yake ganin zai iya rike kasar nan ya kai ta ga ci idan har aka zabe sa.

KU KARANTA: Kar ayi da na sani: Inyamurai za su marawa Buhari baya a 2019

‘Dan takarar na Shugaban kasa yayi Digiri a fannin Akanta a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Bayan nan kuma Ibrahim Dankwambo yayi Digirgir a bangaren tattalin azriki da sauran bangarorin harkar kudi a wasu Jami’o’in Kudancin Kasar nan.

Ibrahim Hassan Dankwambo ya taba rike babban Akanta Janar na Najeriya na tsawon shekaru kusan 6. Bayan nan ne ya ajiye aikin sa ya nemi Gwamnan Jihar Gombe a 2011. A 2019 ne dai wa’adin Gwamnan na Jam'iyyar adawa ta PDP zai kare.

Kwanaki kun ji cewa ‘Yan takarar PDP za su hada karfi wajen tika Shugaba Buhari da kasa. Gwamna Dankwambo da irin Sule Lamido sun tabbatar da cewa za su marawa duk wanda PDP ta ba tuta baya a zaben 2019 domin an doke APC a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel