APC tayi mi'ara koma baya a kan zaben fitar da 'yan takara

APC tayi mi'ara koma baya a kan zaben fitar da 'yan takara

- A satin da ya gabata ne jam'iyyar APC tayi taron kwamitin zartarwa a karo na farko tun bayan ficewar wasu jiga-jigan'ya'yan ta

- Jam'iyyar ta tattauna hanyar da ya kamata su bi domin gudanar da zaben fitar da 'yan takara

- APC na son fitar da 'yan takarar ta hanyar bawa jama'a damar zaben mutumin da suke so ya yi takara

A karshen makon jiya ne jam'iyyar APC mai mulki ta gudanar da taron kwamitin zartarwa (NEC) na kasa domin tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi zaben shekarar 2019 musamman zabukan fitar da 'yan takara.

APC tayi mi'ara koma baya a kan zaben fitar da 'yan takara

APC tayi mi'ara koma baya a kan zaben fitar da 'yan takara
Source: Depositphotos

A karshen taron nata, APC ta amince cewar zata gudanar da zaben fitar da dan takarar shugaban kasa ta hanyar amfani da daliget yayin da jama'a zasu zabi ragowar 'yan takarar.

DUBA WANNAN: Kayar da Buhari ba shine zai magance matsalar Najeriya ba - Fani Kayode

Sai dai a wani mataki da za a iya kira da mi'ara koma baya, jam'iyyar APC ta canja matakin da ta dauka wancan satin tare da sanar da cewar yanzu zata gudanar da zaben 'yan takarar ne ta hanyar da jama'a suka fi sani da kato bayan kato.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron NEC, Simon Lalong, gwamnan jihar Filato, ya bayyana cewar duk jihar da ba ta son gudanar da zabukan fitar da 'yan takara ta hanyar da jam'iyyar ta amince, dole su aiko a rubuce domin neman izinin uwar jam'iyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel