Gwamnatin Buhari ta samu Biliyan 118 cikin watan guda ta hannun Kwastam

Gwamnatin Buhari ta samu Biliyan 118 cikin watan guda ta hannun Kwastam

Labari ya zo mana cewa Hukumar fasa kwauri na kasa karkashin Shugaban ta Hameed Ali ta samu makudan kudin da ba ta taba samu ba a cikin wata guda a tarihin Hukumar ta kwastam ta Najeriya.

Gwamnatin Buhari ta samu Biliyan 118 cikin watan guda ta hannun Kwastam

Shugaban Hukumar Kwastam na kasa Hameed Ali mai ritaya
Source: Original

A watan Agustan da ta wuce, Hukumar kwastam ta samu sama da Naira Biliyan 100. Jaridar The Nation ta kasar nan ta rahoto wannan. A tarihin Hukumar dai tun kafuwar ta, ba a taba samun irin wannan kudi a wata guda ba.

Joseph Attah wanda shi ne babban Jami’in Hukumar na yada labarai wayau PRO yace Shugaban Kwastam na kasa Kanal Hameed Ali mai ritaya ne ya bayyana wannan a makon da ya gabata a babban Birnin Tarayya Abuja.

KU KARANTA: Hukumar Kwastam ta kuma hada wasu makudan Miliyoyin Naira

Kwastam ta samu Naira Biliyan 118 a cikin watan jiya tun kafin watan ya kare. Hakan ya yiwu ne a sanadiyyar tsare-tsaren da aka samu na zamani bayan zuwan Hamid Ali wanda ya dage tukuru wajen ganin an maida hankali.

Za ayi amfani da wannan kudi wajen gina abubuwan more rayuwa a fadin kasar nan kamar yadda Gwamnatin Buhari tayi alkawari. A halin yanzu dai farashin gangar man fetur ya rage kudi idan aka kamanta da abin da ake samu a baya.

Jiya kun ji cewa an raba sama da Naira Biliyan 700 watan jiya a Najeriya. Gwamnatin Tarayya da Gwamnoni da Kananan Hukumomi sun raba Biliyan 714 inji Ministar kudi Kemi Adeosun.

.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel