Rundunar soji ta karyata rahoton cewa Boko Haram ta kai hari a sansanin soji dake Borno

Rundunar soji ta karyata rahoton cewa Boko Haram ta kai hari a sansanin soji dake Borno

- Rundunar soji ta karyata rahoton da ke cewa Boko Haram ta kai hari a wani sansanin soji da ke jihar Borno

- Wani jami'in rundunar ya kira labarin da "kanzon kurege"

- A rahoton, an bayyana cewa mayakan Boko Haram, sun kashe akalla sojoji 30 a harin na ranar Alhamis, 30 ga watan Augusta

Rundunar sojin Nigeria, a jiya Asabar, 01 ga watan Satumba, ta ce babu kamshin gaskiya a rahotannin da ake yadawa na sabon harin da kungiyar Boko Haram ta kai a sansanin rundunar soji da ke jihar Borno.

Wani kamfanin dillancin labarai ya kawo rahoton cewa rundunar mayakan Boko Haram sun kai hari a sansanin sojin, inda suka kashe sojoji akalla 30, a ranar Alhamis, 30 ga watan Augusta.

A rahoton, an bayyana cewa dakarun rundunar ta Boko Haram, sun juya keyarsu don neman tsira da rayukansu bayan da rundunar sojin ta samu agaji daga wasu sojoji da kayan yakin da aka kawo.

KARANTA WANNAN: Shuwagabannin duniya na jerin gwano don ganawa da Buhari duk da Trump ya kirashi 'maras tagomashi

Sai dai, da aka tuntube shi don sanin sahihancin labarin, wani jami'i daga rundunar sojin ya karyata faruwar wannan lamari.

Ya ce: "Don Allah, ina ne kuka samo wannan labarin kanzon kuregen?"

Rundunar soji ta karyata rahoton cewa Boko Haram ta kai hari a sansanin soji dake Borno

Rundunar soji ta karyata rahoton cewa Boko Haram ta kai hari a sansanin soji dake Borno
Source: Depositphotos

A wani labarin kuwa:

Kungiyar dake kare muradun shugaban kasa Muhammadu Buhari, G-23, ta ce kabilar Igbo ba zata sake yin dambarwar da tayi a zaben 2015 ba, inda ta zabi yin siyasar kabilanci mai maikon zaben cancanta, kamar dai yadda ta zabi tsohon shugaban kasa Jonathan kawai saboda bangarancin shiyya.

Kungiyar ta nuna damar abubuwan da suka faru a wancan lokacin, da suka shafi siyasar Kudu maso Gabashin kasar, inda ta ce kabilar Igbo zasu fito kwansu da kwarkwatarsu don marawa Buhari baya, na yin tazarce a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel