Yanzu-yanzu: Coci ya rubza da masu bauta da safen nan

Yanzu-yanzu: Coci ya rubza da masu bauta da safen nan

- Ginin babban coci a jihar Delta ya rikito kan masu bauta

- Akalla mutum daya ya rasa rayuwarsa

Ginin cocin St. Paul Catholic Church, Ugolo, Adagbrasa da ke karamar hukumar Okpe na jihar Delta ya rubza da masu bauta da safen yau Lahadi, 2 ga watan agusta 2019 yayinda suke bauta.

An tabbatar da labarin cewa mutum daya ya rasa ransa kuma da yawa sun jikkata.

Jaridar Daily Trust ta samu rahoton cewa gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya umurci wata tawaga karkashin jagorancin kwamishanan ayyukan jihar, Cif James Augoye, su tafi inda wannan abu ya faru domin gano ainihin abinda ya faru a cocin.

A wata jawabi da sakataren yada labaran gwamnan, Mr Charles Aniagwu, ya siffanta wannan annoba a matsayin abin takaici da ban tsoro.

Gwamnan ya nuna juyayinsa ga mutum daya da aka rasa, kana ya umurci tawagar gwamnatin ta duba yadda za'a taimakawa wadanda suka jikkata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel