Ambaliyar ta salwantar da rayukan Mutane 14 a jihar Neja

Ambaliyar ta salwantar da rayukan Mutane 14 a jihar Neja

Da sanadin wani rahoto da shafin jaridar The Nation ta ruwaito, hukumar bayar da agajin gaggawa ta bayyana cewa, ambaliyar ruwa ta salwantar da rayukan mutane 14 cikin sassa daban-daban na fadin jihar Neja dake Arewacin Najeriya.

A yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Minna a ranar Asabar ta yau, shugaban hukumar, Alhaji Garba Salisu ya bayyana cewa, hukumar tare da agajin Sarakan Ruwa kimanin 200 na yankin sun bazama cikin aikin ceto a yankunan da ambaliyar ruwa ta auku.

Ambaliyar ta salwantar da rayukan Mutane 14 a jihar Neja

Ambaliyar ta salwantar da rayukan Mutane 14 a jihar Neja
Source: Depositphotos

Shugaban hukumar ya kuma nemi al'ummar jihar akan kauracewa gina gidaje a hanyoyi da magudanan ruwa tare da gargadinsu kan illar zubar da shara a wuraren da ba su dace ba da hakan zai taimaka wajen rage aukuwar wannan annoba.

KARANTA KUMA: Ana adawa da Buhari ne kawai saboda kare talakawansa - RBM

Ya kuma yi kira ga al'ummomin dake zaune a yankuna masu yiwuwa ta aukuwar amabaliya akan su karaucewa yakunansu zuwa wani lokaci domin gujewa wannan mummunar annoba.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne ambaliyar ta yi babbar barna cikin wasu kananan hukumomi 8 a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel