Ban taba fita PDP ba: Sule Lamido ya roke 'yan jam'iyya suyi masa halacci

Ban taba fita PDP ba: Sule Lamido ya roke 'yan jam'iyya suyi masa halacci

- Sule Lamido ya roke 'yan jam'iyya suyi masa halacci

- Yace yana cikin wadan da suka kafa jam'iyyar a 1998

- Yace shi bai taba fita daga jam'iyyar ba

Daya daga cikin fitattun 'yan siyasar Najeriya dake neman tikitin takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP Alhaji Sule Lamido ya roki 'yan jam'iyyar da su yi masa halacci musamman ma shi da bai taba fita daga jam'iyyar ba.

Ban taba fita PDP ba: Sule Lamido ya roke 'yan jam'iyya suyi masa halacci

Ban taba fita PDP ba: Sule Lamido ya roke 'yan jam'iyya suyi masa halacci
Source: Facebook

KU KARANTA: Rashawa: EFCC ta taso wani Sanatan PDP gaba

Alhaji Sule yayi wannan rokon ne a lokacin da yake zantawa da jiga-jigan jam'iyyar da za su gudanar da zaben fitar da gwani na jihar Nasarawa a cigaba da yawon zumuncin da yake yi.

Legit.ng ta samu cewa Sule da yake jawabi a wajen taron, ya kara da cewa yana daga cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar ta PDP a shekarar 1998 kuma tun lokacin har yanzu bai taba fita ba.

Jam'iyyar ta PDP dai yanzu haka mutane da dama sun nuna sha'awar su ta neman tikitin ta domin shiga zabukan gama gari da za'a gudanar a shekarar 2019 da suka soma sayar da fom din.

A wani labarin kuma, Sanata Kabiru Garba Marafa dake wakiltar mazabar jihar Zamfara ta tsakiya a zauren majalisar dattawan Najeriya ya yi hasashen tunkarowar babbar matsala a jam'iyyar su ta APC idan dai har bata bi tsarin gudanar da zaben fitar da gwani na kato-bayan-kato ba.

Sanatan dai wanda ke neman tikitin jam'iyyar don yin takarar gwamna a jihar ya ce idan har jam'iyyar tayi fatali da tsarin a matakin jahohi to ta shirya zuwa kotu da ma faduwa zabe a shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel