Da dumin sa: Wani gwamnan ya shiga taron sirri da hadiman sa, yana shirin ficewa daga APC

Da dumin sa: Wani gwamnan ya shiga taron sirri da hadiman sa, yana shirin ficewa daga APC

- Gwamnan Jihar Legas na shirin fita daga APC

- Ance yana can yana wata ganawar sirri da mukarraban sa

- Ana rade-raden sun bata da Bola Tinubu

Labarin da ke iso mana yanzu na nuni ne da cewa Gwamnan jihar Legas, Mista Akinwunmi Ambode yanzu haka ya cikin wani gagarumin taron sirri da dukkan mukarraban sa a gidan gwamnatin jihar da ke a unguwar Ikeja.

Da dumin sa: Wani gwamnan ya shiga taron sirri da hadiman sa, yana shirin ficewa daga APC

Da dumin sa: Wani gwamnan ya shiga taron sirri da hadiman sa, yana shirin ficewa daga APC
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Dubun wani dan damfara a Fezbuk ta cika

Majiyar mu dai ta samu labarin cewa taron da ya kira yana da alaka ne da maganar fitar sa daga jam'iyyar APC mai mulki biyo bayan matakin da ta dauka na gudanar da zabukan fitar da gwani na kato-bayan-kato.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa gwamnan dai yana shirin raba gari ne da jagoran jam'iyyar a jihar Cif Bola Ahmad Tinubu bayan zargin da yake yi na cewa tsohon gwamnan baya son ya zarce.

Yanzu haka dai ana ta rade-raden cewa gwamnan na tunanin komawa daya daga cikin jam'iyyun Peoples Democratic Party, PDP, ko Action Democratic Congress, ADC da ke da goyon bayan Cif Olusegun Obasanjo.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Delta dake ke kudu maso kudancin Najeriya Cif Ayiri Emami ya yi ikirarin cewa dayawa daga cikin wadanda ke zagaye da Shugaba Buhari sune ke dagula masa lissafi.

Cif Ayiri yace musamman ma ministocin gwamnatin Shugaba Buhari kwata-kwata basu don suka cigaban sa kuma a lokutta da dama sukan zamo tamkar 'yan hana ruwa gudu a sha'anin tafiyar da gwamnatin ta sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel