Ni na san abinda zai faru idan na rasa tikitin tsayawa takara a PDP - Kwankwaso

Ni na san abinda zai faru idan na rasa tikitin tsayawa takara a PDP - Kwankwaso

- Kwankwaso ya ce zai ci gaba da kasancewa a jam'iyyar PDP ko da kuwa bai samu tikitin tsayawa takar shugabancin kasa na jam'iyyar ba

- Ya kuma goyi bayan kudirin jam'iyyar na zabar dan takarar shugaban kasa ajam'iyyar ba tare daanyi zaben fitar da gwani ba

- Sai dai, ya jaddadawa jam'iyyar muhimmancin baiwa dan Arewa-maso-Yamma tikitin tsayawa takarar shugabancin kasar

Tsohon gwamnan jihar Kani kuma mai son tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce zai cigaba da zama a cikin jam'iyyar tare da yin duk mai yiyuwa don ta samu nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Kwankwaso wanda ya karbi takardar tsayawa takarar shugaban kasa a PDP a ranar Juma'a, 31 ga watan Augusta, a sakatariyar jam'iyyar ta kasa dake Abuja, ya kuma shaidawa manema labarai cewa idan har jam'iyyar ta amince da tsaida dan takara mafi dacewa to zai amince da sakamakon zaben fitar da gwanin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Kwankwaso yana cewa shine ya zamo na biyu a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a 2015, amma bai ce uffan akan yadda jam'iyyar ta daukeshi a yanzu ba.

KARANTA WANNAN: PDP ta bayyana dalilin tilasta Saraki, Tambuwal, da sauransu sa hannu a takardar rantsuwa

Ni na san abinda zai faru idan na rasa tikitin tsayawa takara a PDP - Kwankwaso

Ni na san abinda zai faru idan na rasa tikitin tsayawa takara a PDP - Kwankwaso
Source: Twitter

Ya ce: "Bana tunanin wani abu zai faru idan aka ce ban samu nasara a zaben fitar da gwani ba"

Da yake amsa tambaya game da yunkurin da PDP ta keyi na zabar wanda zai tsaya takara ba tare da yin zaben fitar da gwani ba, , Kwankwaso ya ce: "Zabar wanda ya dace kai tsaye shine ya fi dacewa ayi, amma da yawan wasu yan takarar sunfi ganin cewa ayi 'yar tinke.

Idan har shuwagabannin jam'iyyar suka ce ga wanda suke so ya tsaya takara, to ni bani da matsala da hakan, zan amince da hukuncin da suka yanke"

Sai dai, ya jaddadawa jam'iyyar muhimmancin baiwa dan Arewa-maso-Yamma tikitin tsayawa takarar shugabancin kasar.

A baya dai Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan,ya baiwa yan takara a jam'iyyar ta PDP tabbacin yin sahihin zaben fitar da gwani, wanda kowa zai amince da shi.

Ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Atahiru Bafarawa, a ranar juma'a, 31 ga watan Augusta, a ofishinsa dake Yenagoa.

Jonathan ya ce idan har aka gudanar da sahihin zaben fitar da gwani, zai baiwa wadanda basu samu nasara ba damar marawa masu nasara baya, ba tare da jin zafi ba, don ganin jam'iyyar ta samu nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel