Ana adawa da Buhari ne kawai saboda kare talakawansa - RBM

Ana adawa da Buhari ne kawai saboda kare talakawansa - RBM

Wata kungiya mai fafutika da kuma goyon bayan tazarcen Buhari ta RBM, Re-elect Buhari Movement, ta bayyana cewa mafi akasarin mutane na adawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kawai domin jajircewar sa ta kare talakawa.

Kungiyar take cewa, masu adawa da hamayya da shugaban kasa Buhari na aikata hakan ne kadai sakamakon akidu da tsare-tsaren sa na damuwa da bukatun talakawan kasar nan.

A cewar kungiyar, wasu daga cikin 'yan siyasa da masu hannu da shuni na kasar nan na adawa da shugaban kasar ne kadai sakamakon dakile masu duk wata hanya ta wawuson dukiyar al'umma da ta sanya suke kai ruwa rana ta ganin bai koma kan kujerar sa ba a babban zaben na 2019.

An adawa da Buhari ne kawai saboda kare talakawansa - RBM

An adawa da Buhari ne kawai saboda kare talakawansa - RBM
Source: UGC

Cikin wata sanarwa a ranar Juma'ar da ta gabata da sanadin jagoran kungiyar, Mista Emmanuel Umohinyang ya bayyana cewa, duk da irin hamayya gami da hare-hare, al'ummar Najeriya za su jefawa shugaba Buhari kuri'un su domin ya ci gaba da wannan kyakkyawan aiki.

KARANTA KUMA: 'Yan Siyasa 8 da ake zargi da rashawar N232bn kuma suke fafutika akan tazarcen Buhari

Mista Emmanuel ya kuma yabawa shugaba Buhari dangane da kwazon sa na jajircewa kan managarcin shugabanci tare da kyautata ma sa zato akan ci gaba dorewa akan hakan na damuwa da talakawansa.

Ya kara da cewa, an samu kyakkyawan sauyi tun yayin da shugaba Buhari ya karbi ragamar mulki a kasar nan dake ci gaba da habaka da kawo ci gaba sakamon tudun tsira da al'ummar suka hanga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel