PDP ta bayyana dalilin tilasta Saraki, Tambuwal, da sauransu sa hannu a takardar rantsuwa

PDP ta bayyana dalilin tilasta Saraki, Tambuwal, da sauransu sa hannu a takardar rantsuwa

- PDP ta ce dukkanin wadanda zasu tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar dole su sa hannu a takardar rantsuwa

- Takardar rantsuwar zata sanar da masu tsayawa takarar abubuwan da jam'iyyar ta ke bukata daga wajensu, a yayin zaben fitar da gwani da kuma bayan kammalawa

- Rantsuwar zata tilasta dukkanin yan takarar amincewa da sakamakon zaben fitar da gwani da jam'iyyar zata gudanar a wannan watan

Jam'iyyar PDP ta bayyana dalilinta na umurtar kafatanin masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar da sanya hannu a wata takardar rantsuwa gabanin zaben fitar da gwani na jam'iyyar dake gabatowa.

Takardar rantsuwar zata sanar da masu tsayawa takarar abubuwan da jam'iyyar ta ke bukata daga wajensu, a yayin zaben fitar da gwani da kuma bayan kammalawa.

Shuwagabannin jam'iyyar sun ce takardar rantsuwar zata tabbatar da ganin cewa yan takarar sun bi dukkanin matakai da sharuddan da jam'iyyar ta tanadar.

PDP ta bayyana dalilin tilasta Saraki, Tambuwal, da sauransu sa hannu a takardar rantsuwa

PDP ta bayyana dalilin tilasta Saraki, Tambuwal, da sauransu sa hannu a takardar rantsuwa
Source: UGC

KARANTA WANNAN: 'Yan Siyasa 8 da ake zargi da rashawar N232bn kuma suke fafutika akan tazarcen Buhari

Sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar a matakin kasa, Kola Ologbondiyan, a cikin wata sanarwa da jaridar Punch a ranar juma'a, 31 ga watan Augusta, ya ce tuni an sanar da dukkanin yan takarar akan bukatar mallakar littafin Dokoki da Oda na jam'iyyar gabanin zaben fitar da gwani.

Ya ce: "Tuni jam'iyyar ta fara shirya littafin, wanda zai zama tilas ga dukkanin yan takarar mallakarshi, don basu damar sa hannu akan yarjejeniyar amincewa da sakamakon zaben fitar da gwani da kuma abubuwan da jam'iyyar take bukata daga garesu gabani da kuma bayan kammala zaben.

"Sai dai ina so in sanar da jama'a cewa, jam'iyyar ba wata kafa bace ta kaddamar da doka. Muna son gudanar da zabe ne cikin aminci, gaskiya da kuma gudanar da sahihin zaben fitar da gwani, wanda zai karbu ga jam'iyyar, yan takara da kuma jama'ar kasar."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://business.facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel