Da dumi dumi: PDP ta bukaci wasu yan takar shugaban kasa a jam'iyyar da su janye kudurinsu - Majiya

Da dumi dumi: PDP ta bukaci wasu yan takar shugaban kasa a jam'iyyar da su janye kudurinsu - Majiya

- PDP ta bukaci wasu daga cikin masu neman tsayawa takara a jam'iyyar, da su janye kudirinsu don baiwa nagartattu dagacikinsu dama

- A cewar wata majiya daga PDP, shuwagabannin jam'iyyar na kasa ne suka bayyana wannan bukatar a zaman da sukayi da kafatanin yan takarar

- Haka zalika, jam'iyyar PDP ta umurci yan takarar da sa hannu a takardar yarjejeniya na amincewa da sakamakon zaben fitar da gwani na jam'iyyar

Rahotanni da muke samu a yanzu na nuni da cewa akwai wasu daga cikin masu neman takarar shugabancin kasar a zaben 2019, karkashin jam'iyyar PDP, da ka iya janye wannan kudiri nasu kafin ranar zaben fitar da gwani na jam'iyyar da zai gudana a wannan watan.

Wata majiya daga PDP ta shaidawa kamfanin jarida na Punch cewa shuwagabannin jam'iyyar na kasa sun yi wani zama da masu neman tsayawa takarar shugabancinnkasar a jam'iyyar, inda suka shaida masu cewa akwai bukatar wasu daga cikinsu su janye, don bada dama ga zakakuran cikinsu.

A cewa majiyar, an kuma umarci yan takarar shugabancin kasar, da su sanya hannu a takardar amincewa da duk wani sakamako da jam'iyyar ta fitar na zaben fitar da gwani, don gujewa rabuwar kawuna bayan kammala zaben.

KARANTA WANNAN: Tafiyar Buhari 'Kasar Sin wata kitimurmura ce ta ƙulla maguɗin Zaɓe da tsige Saraki - Frank

"Shuwagabannin jam'iyyar na kasa sun zauna da masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar, inda aka sanar da su cewa wasunsu dole su janye daga takarar don bada dama ga zakakurai a cikinsu, da zasu iya jan daga da shugaba Buhari a 2019.

"Don haka, ana sa ran da yawa daga cikinsu zasu janye daga tsayawa takarar a wannan watan. Haka zalika an umurce su da sanya hannu akan takardar yarjejeniya, kan amincewa da sakamakon zaben fitar da gwani."

Akalla mutane 10 ne suka sayi takardar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, da suka hada da: Atiku Abubakar, Sule Lamido, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, Ahmed Makarfi, Ibrahim Hassan Dankwambo da kuma, Attahiru Bafarawa.

Sauran sun hada da: Kabiru Tanimu Turaki, Datti Baba-Ahmed, Senator Bukola Saraki, Aminu Waziri Tambuwal da dai sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel