Da duminsa: Balarabe Musa ya ajiye shugabancin jam'iyyar PRP

Da duminsa: Balarabe Musa ya ajiye shugabancin jam'iyyar PRP

- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa, ya ajiye mukaminsa na shugabancin jam'iyyar PRP na kasa

- Balarabe Musa ya bayyana cewar ya ajiye shugabancin jam'iyyar ne domin bawa matasa dama saboda rashin lafiya da yake fama da ita

- Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne jiya juma'a yayin taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa, ya ajiye mukaminsa na shugabancin jam'iyyar PRP na kasa.

Da yake bayyana wannan mataki da ya dauka a jiya Juma'a yayin taron jam'iyyar a Kaduna, Mista Musa ya ce ya ajiye mukamin ne domin bawa matashi damar cigaba da rikon jam'iyyar saboda rashin lafiyar dake damunsa.

Da duminsa: Balarabe Musa ya ajiye shugabancin jam'iyyar PRP

Da duminsa: Balarabe Musa ya ajiye shugabancin jam'iyyar PRP
Source: Depositphotos

Mista Musa ya sanar da hakan ne a wurin taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar da aka gudanar jiya a Kaduna.

DUBA WANNAN: Wata mace Kirista ta zama gwamna a kasar Misra a karon farko

Tsohon gwamnan ne ya kafa ta PRP bayan dawowar mulkin dimokradiyya a shekarar 1999 domin cigaba da raya jam'iyyar da a cikinta ne aka zabe shi gwamnan jihar Kaduna a shekarar 1979.

Sai dai ya bawa daukacin 'yan jam'iyyar tabbacin cewar zai cigaba da zama a cikinta.

"Ya zamar min dole na ajiye shugabancin jam'iyyar mu ta PRP saboda karfina ya ragu kuma ga shi ina fama da rashin lafiya. Ya kamata na bawa masu karfi a jiki da koshin lafiya dama," a cewar Mista Musa.

Ya kara da cewar wanda zai gaje shi ba wai zai kasance matashi kawai ba, tilas ya zama mai kishi da basirar ciyar da jam'iyyar ta PRP gaba.

Kazalika ya bayyana cewar jam'iyyar zata kammala zabukan cikin gida na fitar da 'yan takara kafin kurewar wa'adin da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel