Sojin Najeriya sun yi wa 'yan Boko Haram 'ruwan wuta' a Zari, kalli bidiyon

Sojin Najeriya sun yi wa 'yan Boko Haram 'ruwan wuta' a Zari, kalli bidiyon

Rundunar Operation Lafiya Dole ta sanar da cewa, a jiya a ranar Alhamis, 30 ga watan Augusta, dakarun Sojin Saman Najeriya sun yiwa mayakan Boko Haram ruwan bama-bamai inda su kayi nasarar lalata motoci masu dauke da bindiga 2 tare da hallaka 'yan ta'adda da dama a garin Zari da ke kusa da tafkin Chadi a jihar Borno.

Sakon da ya fito daga bakin Kakakin rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya ce sojin sun kai samamen na bayan an gano 'yan ta'adan sun buya a karkashin wasu bishiyoyi kilomita 5 Kudu maso yammacin Zari bayan arangama da Sojin Najeriya a Zari.

Sojin Najeriya sun yi wa 'yan Boko Haram 'ruwan wuta' a Zari, kalli bidiyon

Sojin Najeriya sun yi wa 'yan Boko Haram 'ruwan wuta' a Zari, kalli bidiyon
Source: Facebook

Sojin sunyi amfani da jiragen yaki kirar Alpha JET, F-7 da jiragen yaki masu saukan ungulu kirar Mi-35M wajen yiwa 'yan ta'addan luguden wuta a wuraren da suke buya.

DUBA WANNAN: Wata mace Kirista ta zama gwamna a kasar Misra a karon farko

Kamar yadda bidiyon ya nuna, za'a lura cewa sauran 'yan ta'addan da bama-baman basu hallaka ba sun tarwatse bayan harin da aka kai musu. Daga bisani dakarun Sojin Najeriya sun kara kai wata harin ta kas domin karasa wadanda su kayi saura.

Kalli bidiyon a kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel