'Yan Bindiga sun yi awon gaba da wani manemin takarar Kujera a Majalisar Wakilai

'Yan Bindiga sun yi awon gaba da wani manemin takarar Kujera a Majalisar Wakilai

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito mun samu rahoton cewa, wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani manemin takarar kujera a majalisar wakilai ta mazabar Abi da Yakkur ta jihar Cross River, Jerome Egbe, a babban birnin jihar na Calabar.

Wani mashaidin wannan ta'addanci, Cyprian Ido, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 11.00 na safiyar ranar Alhamis din da ta gabata a wani Garejin Kanikawa dake unguwar Asari Iso ta birnin Calabar.

Mista Ido ya bayyana cewa, 'yan bindigar sun yi awon gaba da Mista Egbe ne cikin wata bakar Mota kirar Hilux bayan sun lakada ma sa dukan tsiya sakamakon gardama da ya yi masu.

'Yan Bindiga sun yi awon gaba da wani manemin takarar Kujera a Majalisar Wakilai

'Yan Bindiga sun yi awon gaba da wani manemin takarar Kujera a Majalisar Wakilai
Source: Facebook

A yayin tabbatar da wannan lamari, kakakin 'yan sandan jihar, Irene Ugbo, ya bayyana cewa hukumar tuni ta fantsama cikin bincike domin tabbatar da ceto Mista Egbe cikin gaggawa.

KARANTA KUMA: Masana'anta ita ce mabuɗin haɓakar tattalin arziki - Halima Dangote

Rahotanni sun bayyana cewa, Mista Egbe malami ne a jam'iar Kimiya ta jihar Cross River wanda ya rike kujera ta shugabancin kungiyar 'daliban jami'o'in Najeriya a lokutan baya.

Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunan ta ta bayyana cewa, akwai yiwuwar daya daga cikin abokan hamayyar sa na siyasa ke da hannu cikin wannan aika-aika.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel