Ta bayyana: An sauke shugabannin PDP a jihar Kano ne don baiwa Kwankwaso shugabancin jam'iyyar a Jihar

Ta bayyana: An sauke shugabannin PDP a jihar Kano ne don baiwa Kwankwaso shugabancin jam'iyyar a Jihar

Kwamitin gudanarwan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP, ta sauke dukkan shugabannin jam'iyyar na jihar Kano.

Jaridar Daily Nigerian ta tattaro cewa shugabannin jam'iyyar PDP ta kasa sunyi hakan ne domin baiwa tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takaran kujeran shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso, daman juya jam'iyyar.

A waa jawabi da kakakin jam'iyyar ta kasa, Kola Ologbondiyan, ya saki a yau Juma'a, 31 ga watan Agusta 2018, ya ce an sauke dukkan shugabannin daga yanzu.

Jawabin ta bayyana cewa kwamitin gudanarwan jam'iyyar ta yanke wannan shawara ne ranan Alhamis, 30 ga watan Agusta.

Jawabin yace: "Saboda haka, an nada sabuwar kwamitin rikon kwarya domin shugabantan jam'iyyar a jihar. Za'a saki sunayen sabbin shugabannin ba da dadewa ba."

"Ana kira ga dukkan mambobin jam'iyyar na jihar Kano da kuma kasa ga baki daya sun sanda wannan mataki da aka dauka."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel