PDP ta dakatar da jami’an jamiyyar na jihar Kano

PDP ta dakatar da jami’an jamiyyar na jihar Kano

- Jam'iyyar PDP ta dakatar da jami'anta na reshen jihar Kano

- An kafa kwmitin rikon kwarya da zai kula daharkokin jam'iyyar

Kwamitin aiki na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa ta tarwatsa kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar reshen jihar Kano.

Wata sanarwa daga babban sakataren labaran jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan a ranar Juma’a, 31 ga atan Agusta ya bayyana cewa dakatarwan ya fara aiki ne a take.

PDP ta dakatar da jami’an jamiyyar na jihar Kano

PDP ta dakatar da jami’an jamiyyar na jihar Kano
Source: Depositphotos

Sanarwan ya bayyana cewa an yanke wannan shawarar ne bayan ganawar kwamitin masu ruwa da tsaki najam’iyyar wadda aka gabatar a ranar Alhamis.

KU KARANTA KUMA: Jirgin Shugaba Buhari ya bar Abuja inda ya shilla zuwa kasar China (hotuna)

“Yanzu haka an kafa kwamitin rikon kwarya da zatatafiyar da harkokin jam’iyyar reshen jihar.

“Za’a sanar da jama’a cikakken bayani akan kwamitin rikon kwaryan a lokacin da ya kamata."

A wani lamari na daban mun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya koka kan kalubalen da kasar ke fuskanta yaynda kungiyoyi da dama suka siya tare da gabatar masa da fam din tsayawa takara shugabancin kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya sosa ran tsohon mataimakin shugaban kasarlokacin da wata mai suna Princess Adekem Adesanya ta gabatar da jawabinta akan kalublen da kasar ke fuskanta a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel