Jirgin Shugaba Buhari ya bar Abuja inda ya shilla zuwa kasar China (hotuna)

Jirgin Shugaba Buhari ya bar Abuja inda ya shilla zuwa kasar China (hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 31 ga watan Agusta ya bar Abuja zuwa Beijing, Cina domin halartan taron hadin gwiwar China-Afrika (FOCAC).

Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari zai kai wannan ziyarar ne don halartar taron majalisar koli na bakwai na hadin kan kasashen nahiyar Afirka da kasar China, FOCAC da zai gudana a babban brinin Beijing daga ranakun 3 zuwa 4 ga watan Satumba.

Shugaba Buhari zai samu rakiyar uwargidansa, Aisha zuwa Beijing inda anan ne za’agabatar da taron a babban dakin taron Great Hall.

Jirgin Shugaba Buhari ya bar Abuja inda ya shilla zuwa kasar China (hotuna)

Jirgin Shugaba Buhari ya bar Abuja inda ya shilla zuwa kasar China
Source: Twitter

Har ila yau daga cikin masu yiwa shugaban kasar rakiya akwai Gwamna Mohammed Abubakar, Akinwumi Ambode, Mohammed Badaru, da Rochas Okorocha, sai kuma Sanatoci da suka hada da Abdullahi Adamu, George Akume, Godswill Akpabio, Aliyu Wammako, da Minisotoci guda 9.

KU KARANTA KUMA: An nada Sani Danja a matsayin jakadan kungiyar NFVCB

Jirgin Shugaba Buhari ya bar Abuja inda ya shilla zuwa kasar China (hotuna)

Jirgin Shugaba Buhari ya bar Abuja inda ya shilla zuwa kasar China
Source: Twitter

Bayan bude wannan taro, shugaba Buhari zai gana da shugaban kasar China Xi Jin Ping da Firai ministan kasar Li Keqiang, inda zasu tattauna batutuwan da suka shafi hanyar samar da kudaden da za’a aiwatar da wasu manyan ayyuka a Najeriya, tare da tattaunawa akan hanyar kara dankon zumunci tsakaninsu.

Jirgin Shugaba Buhari ya bar Abuja inda ya shilla zuwa kasar China (hotuna)

Jirgin Shugaba Buhari ya bar Abuja inda ya shilla zuwa kasar China
Source: Twitter

Daga karshe Buhari zai yi amfanin da wannan damar ta haduwarsa da shugaba Xi Jin Ping don samun bayanai daga jami’an gwamnatin China game da matsayin ayyukan da suke yi a Najeriya, musamman aikin wutar lantarki da na titunan jirgin kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel