2019: Ban tsayar da kowa ba a kowani mukamin siyasa – Dogara

2019: Ban tsayar da kowa ba a kowani mukamin siyasa – Dogara

- Yakubu Dogara ya karyata rade-radin cewa ya tsayar da wasu yan takara

- Yace hakan baya daga cikin tsarinsa tsayar da wani a matsayi mai neman wwani kujerar siyasa

- An dai zargi Dogara ne da tsayar da wani dan takara kan ya nemi kujerar mazabar Bogoro a majalisar dokokin jihar Bauchi

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara a ranar Juma’a, 31 ga watan Agusta ya karyata ikirarin cewa ya tsayar da wasu yan takara dake neman kujerun mulki.

Yayinda yake martani akan ikirarin cewa ya tsayar da wasu yan takara dake neman kujerar shugabanci a mazabarsa, Dogara ya bayyana rade-radin a matsayin karya da kuma keta.

A wata sanarwa dauke da sa hanun mai bashi shawara na musamman a harkokin labarai, Mista Turaki Hassan wanda aka kuma gabatar ga manema labarai a Abuja, Dogara ya karyata cewar ya taba neman wani yayi takarar kujerar mazabar Bogoro a majalisar dokoki na jihar Bauchi.

2019: Ban tsayar da kowa ba a kowani mukamin siyasa – Dogara

2019: Ban tsayar da kowa ba a kowani mukamin siyasa – Dogara
Source: UGC

“A bisa tsari, bana sanya bakina a irin wannan lamarin. Mazabata da abokan siyasa na sun san haka.

“Ban taba tsayar da kowa ba kuma ban taba neman wani ya tsaya takara a karkashin kowace jam’iyyar siyasa ba,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya yanki fam din takarar shugabancin kasa, yayi alkawarin sake farfado da Najeriya

Yakubu Dogara ya shawarci masu rahoto da su tabbatar da labarai kafin su wallafa shi sannan su bukaci mutane da daina yada jita-jita akan sa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya fara tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki kwana daya bayan ya kaddamar da aniyarsa na tsakarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 mai zuwa.

Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa Saraki da mambobin kungiyar yakin neman zabensa suna Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa a yanzu haka, inda suke tattaunawa da gwamnan jihar, Hon Seriake Dickson.

Legit.ng ta tattaro cewa daga nan tawagar yakin neman zaben zasu tafi Umuahia, babban birnin jihar Abia inda Saraki zai kuma tattauna da Gwamna Okezie Ikpeazu kan kudirinsa na takarar shugabancin kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel