Yanzu Yanzu: Saraki ya gana da Dickson da kuma gwamnonin PDP na kudu maso gabas

Yanzu Yanzu: Saraki ya gana da Dickson da kuma gwamnonin PDP na kudu maso gabas

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya fara tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki kwana daya bayan ya kaddamar da aniyarsa na tsakarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 mai zuwa.

Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa Saraki da mambobin kungiyar yakin neman zabensa suna Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa a yanzu haka, inda suke tattaunawa da gwamnan jihar, Hon Seriake Dickson.

Legit.ng ta tattaro cewa daga nan tawagar yakin neman zaben zasu tafi Umuahia, babban birnin jihar Abia inda Saraki zai kuma tattauna da Gwamna Okezie Ikpeazu kan kudirinsa na takarar shugabancin kasa.

Yanzu Yanzu: Saraki ya gana da Dickson da kuma gwamnonin PDP na kudu maso gabas

Yanzu Yanzu: Saraki ya gana da Dickson da kuma gwamnonin PDP na kudu maso gabas
Source: Twitter

Sannan Saraki zai ya da zango a jihar Enugu inda zai gana da Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi a gidan gwamnati. Nan ne zai zamo wur na karshe da shugaban majalisar dattawan zai ziyarta a ranar Juma’a, 31 ga watan Agusta.

A cewar jaridar ThisDay, Saraki ya so yankar fam din takara a sakatariyar PDP dake Abuja a yau, 31 ga watan Agusta amma aka shawarce shi da ya fara zuwa ga gwamnonin kudu maso gabas sannan ya sanar masu da kudirinsa kafin ya yanki fam din.

Ana sanya ran zai yanki fam din nasa a ranar Litinin, 3 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Balarabe Musa ya sauka daga matsayin shugaban jam’iyyar PRP

Idan zaku tuna kafin yanzu Saraki ya gana tsoffin shugabannin kasa uku akan kudirinsa na takarar shugaban kasa a 2019.

Tsoffin shugabannin da Saraki ya tuntuba sun hada da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida, Olusegun Obasanjo da kuma Goodluck Jonathan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel