Atiku ya yanki fam din takarar shugabancin kasa, yayi alkawarin sake farfado da Najeriya

Atiku ya yanki fam din takarar shugabancin kasa, yayi alkawarin sake farfado da Najeriya

- Atiku Abubakar ya yankin fam din nuna ra'ayin takarar kujerar shugaban kasa a karkashin PDP

- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya sha alwashin sake farfado Najeriya idan dai aka zabe shi

- Kimanin mutane sama da 15 ne ke neman takarar wannan kujera a PDP

Domin shiga sahun zaben 2019, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yanki fam din nuna ra’ayin tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Juma’a, 31 ga watan Agusta.

Atiku wadda ke neman tsayawa takarar shugabancin kasa a inuwar PDP yayi alkawarin sake fadrfadon da Najeriya idan har aka zabe shi.

Atiku ya yanki fam din takarar shugabancin kasa, yayi alkawarin sake farfado da Najeriya

Atiku ya yanki fam din takarar shugabancin kasa, yayi alkawarin sake farfado da Najeriya
Source: Depositphotos

Da yake Magana ta bakin daya daga cikin mambobin kungiyar magoya bayansa, Adai Edwin Adai, Atiku ya bayyana cewa yana da abunda ake bukata don ceto kasar daga halin da take ciki a yanzu, sannan kuma a daura ta kan hanyar ci gaba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, a kokarin ganin an gabatar da zaben fidda gwani na gaskiya da amana, shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa ya gana da ‘yan takarar kujerar shugaban kasa a Abuja a daren ranar Laraba, 29 ga watan Agusta.

Tawagar ta jam’iyyar PDP sun samu jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus. Sauran mambobin da suka halarci wannan ganawar sun hada da kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na kasa da wasu mambobin kungiyar amintattu na jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Balarabe Musa ya sauka daga matsayin shugaban jam’iyyar PRP

Wadanda suka halarci ganawar sun hada da Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Plateau, Jona Jang, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi.

Hakazalika tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso da tsohon ministan ayyuka na musamman, Alhaji Kabir Tanimu Turaki sun hallara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel