Fara wa da iyawa: Wata kungiya da Saraki ya ambata ta nesanta kanta da kaddamar da takarar sa

Fara wa da iyawa: Wata kungiya da Saraki ya ambata ta nesanta kanta da kaddamar da takarar sa

- Saraki ya zayyana wasu abubuwa har guda 8 da suka saka shi yanke shawarar shiga takarar shugaban kasar Najeriya

- Yawan masu neman jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar shugaban kasa ya karu ya zuwa mutane 12, dukkan su daga arewacin Najeriya.

- Tun bayan ficewarsa daga APC ake hasashen cewar Saraki ya fita daga jam’iyyar ne domin yana son yin takarar shugaban kasa

Kungiyar matasa masu fafutikar ganin matasa sun shiga siyasa domin a dama da su (Not Too Young To Run) ta nesanta kanta daga kaddamar da takarar shugaban kasa da Saraki ya yi a karkashin jam’iyyar PDP, a jiya, Alhamis a Abuja.

Saraki ya kaddamar da takararsa a jiyan ne yayin gabatar da jawabi a wurin wani taro da kungiyar ta shirya kuma ta gayyace shi.

Fara wa da iyawa: Wata kungiya da Saraki ya ambata ta nesanta kanta da kaddamar da takarar sa

Saraki
Source: Twitter

Kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta bisa yadda Saraki ya yi amfani da taron da ta shirya domin bayyana kudurinsa na tsaya takarar shugaban kasa tare da sanar da cewar ba don hakan ta shirya taron ba kuma ba don haka suka gayyaci shi, Saraki, ba.

DUBA WANNAN: 2019: Abu 10 da Buhari ya fada a wurin taron APC

A wata takardar sanarwa da jagoran kungiyar, Samson Itodo, ya aike wa jaridar Premium Times, kungiyar ta nuna bacin rai da mamaki a kan abinda Saraki ya aikata na yin amfani da suna da kuma taron kungiyar domin bayyana burinsa na tsayawa takarar shuagaban kasa a PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel