Jami’ar sojojin Najeriya zai fara aiki kafin karshen 2018 - Buratai

Jami’ar sojojin Najeriya zai fara aiki kafin karshen 2018 - Buratai

- Babban hafsan soji, Tukur Buratai yayi karin haske akan jami'ar sojoji

- Ya ce zai fara aiki ne kafin karshen wannan shekara ta 2018

- Makarantar zata hada sojoji da yan farin hula ne

Shugaban hafsan soji, Tukur Buratai ya bayyana cewa jami’ar sojoji zai fara aiki kafin karshen wannan shekarar, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mista Buratai ya fadama kafofin watsa labarai a Abuja a ranar Alhamis, 30 ga watan Agusta cewa jami’ar zata gudanar da darusa a fanni daban-daban sannan kuma cewa za’a kwashi dalibai kaso 30 na sojoji sannan kaso 70 yan farin hula, tare da shugaba dan farin hula.

Jami’ar sojojin Najeriya zai fara aiki kafin karshen 2018 - Buratai

Jami’ar sojojin Najeriya zai fara aiki kafin karshen 2018 - Buratai
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa hukumar soji na tattaunawa da kungiyar makarantun jami’a na kasa da kuma ma’aikatar ilimi na tarayya, hukumar zana jarabarawar shiga jami’a (JAMB) da kuma kungiyar dake bayar da tallafi kudi na ilimi.

“Jami’ar sojoji ya fara kammaluwa. Kafin karshe shekara, jami’ar zai fara aiki, za’a gudanar da fannin karatu daban-daban kuma muna jiran a saki matakan da ya kamata a bi.

KU KARANTA KUMA: Ku sake zaba na a matsayin shugaban kasa a 2019 – Buhari ya roki mata

“Jami’ar zai fi raja’a akan yan farar hula muna sanya ran kungiyar bayar da tallafi ga ilimi zata bayar da kudaden da ake bukata yayinda hukumar sojin zata taka nata rawar ganin da akebukata,” inji Buratai.

A wani lamari na daban, mun ji cewa Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin Shugabna kasa Muhammadu Buhari ta fitar da miliyoyin ýan Najeriya daga kangin talauci a shekaru uku da suka gabata.

Yana martani ne akan jawabin da Firai Minista Theresa May da tace kasar Najeriya ce ke da matalauta mafi yawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel